Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar 23 ga watan Oktobar 2024 ne Nijeriya ta jingine laifukan da take zargin Tigran Gambaryan, shugaban kamfanin Binance wanda aka kama a watan Fabarairun 2024 kuma aka yanke wa hukunci tare da kamfaninsa kan zargin safarar kuɗi da ƙin biyan haraji da haifar da karya darajar Naira a Nijeriya.
Lauyar hukumar EFCC, R.U. Adaba, ne ya shaida wa mai shari’a, Emeka Nwite, cewa sun janye ƙarar da suka shigar da Mista Gambaryan saboda dalilai na diflomasiyya.
Sai dai lauyar ba ta yi wani ƙarin haske ba. Ta dai bayyana rashin lafiyar Mista Gambaryan a matsayin dalilin ajiye zargin zarge-zargen da suke yi masa. Bayan sakinsa daga gidan yarin Kuje, sai jami’an Amurka suka shirya masa tafiya ta gaggawa a wannan ranar zuwa Amurka.
Manhaja ta gano cewa, kafin ranar 23 ga Oktobar 2024 da aka yi zama na ƙarshe kan shari’ar shugaban kamfanin Binance, an sha tattaunawar diflomasiyya ta bayan fage tsakanin Nijeriya da Amurka. Wasu majiyoyi masu tushe sun bayyana wa wakilanmu cewa a makon da za a yi zaman ƙarshe na shari’ar, wasu manyan jami’an gwamnatin ƙasar Amurka ciki har da tsohon shugaban ƙasar Joe Biden, sun yi ta ƙoƙarin ganin an saki Mista Gambaryan, ta hanyar turo saƙonni da kiraye-kirayen wayoyi da taruka ta inatanet. Sai fa a ƙarshe aka ƙulla yarjejeniya.
A lokacin da muka fara samun labarin abin da ke faruwa, labarin bai fito ba ƙarara, amma daga baya da muka cigaba da tattaunawa da waɗanda suke kusa da lamarin da kuma dudduba takardu, a yanzu Manhaja tana da cikakken bayani game da yadda matsin lamba ya tilasta wa Nijeriya sakin Mista Gambaryan wanda yin duniya ta hana ba da belinsa na tsawon watanni.
Mista Gambaryan, wanda shi ne shugaban kamfanin Binance kuma shugaban sashen kula da laifukan kuɗi tare da Nadeem Anjarwalla, shugaban kula da sashen mausayar kuɗin Kifto na nahiyar Afirka an yi nasarar tsare su ne a ranar 26 ga watan Fabarairun, 2024 kan rashin bin doka da ba da haɗin kai ga jami’an tsaron Nijeriya da ke bincike kan yadda kuɗin Kirifto ke barazana ga tattalin arziƙin Nijeriya wanda ya jawo wa yankin nahiyar Afirka ta yamma a asara.
Nijeriya ta ce kamfanin Kirifto na Binance ya yi hada-hadar kuɗi da ta kai Dalar Amurka biliyan 21.6 a cikin gida a shekarar 2023. a cikin bayanan da Nijeriya ta samu gani, an zargi kamfanin da da cewa ya ƙi bin umarnin kotu na miƙa wasu muhimman bayanai ga mahukunta.
“Sakamakon ƙin ba da haɗin kai ga mahukunta a Nijeriya, wannan kamfani ba kaɗai ya kauce wa biyan haraji ba ne, akwai yuwuwar sa hannunsa wajen hada-hadar haramtattun kuɗaɗe,” a cewar kundin. “Kuma wannan abu ne da ke yi wa tattalin arziƙin Nijeriya da tsaro barazana.”
Hukumar EFCC da Hukumar karɓar haraji (FIRS) sun shigar da shugabannin kamfanin ƙara kowanennsu a gaban kotu tare da bayyana dalilin ɗaukar matakin da ƙoƙarin kare Nijeriya daga laifuka da suka shafi kuɗi da kiyaye tattalin arziƙin ƙasar daga barazanar hada-hadar kuɗi ta intanet da ɗaukar nauyin ta’addanci da safarar haramtattun kuɗi.
Sai dai ba ba ɗau wani lokaci ba da fara binciken da mahukuntan Nijeriya ke yi, sai gwamnatin Amurka ta fara matsa mata lamba kan ta saki Mista Gambaryan tare da iƙirarin cewa tsohon jami’inta ne na farin kaya. Da fari matsin lamabar ta fara ne da jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills Jr., wanda ya aike wa da ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya takarda kan a saki Gambaryan daga inda yake tsare saboda lamari na jinƙan ɗan’adam.
Sannan Jakadan ya yi ta tuntuɓar ofishin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da ofishin ministan kuɗi da fadar shugaban ƙasa.
“Jakadan bai damu da cewa ana zargin Gambaryan da ma’aikatansa ne da laifuka dabn-daban ba da suka haɗa ƙin biyan haraji da safarar haramtattun kuɗi, abin da kawai ya dame shi shi ne a saki Gambaryan saboda shi ɗan ƙasar Amurka ne” kamar yadda wata majiya ta shaida wa Manhaja. “Kwata-kwata ba sa mutunta tsarin shari’ar ƙasar nan.”
A yayin da Nijeriya ta yi tsayuwar gwamen jaki kan lallai sai Gambaryan ya fuskanci shar’a, sai jakadan ya yi gaggawar sanar da fadar Amurka da sauran hukumomin ƙasar.
A wani taro da aka yi a ba bban birnin Amurka, a watan Mayun 2024, sakataren Amurka, a wancan lokaci, Anthony Blinken, ya nuna tattauna batun da ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar. A ƙarshen watan Afirilu, mataimakin sakataren Amurka, Kurt Campell, ya tattauna batun da Nuhu Ribado a yayin wani taro.
Sannan shi ma mataimakin sakataren Amurka na Nahiyar Afirka, Molly Phee da daraktan hukumar FBI, Christopher Wray, wanda da kansa ya zo Nijeriya a ranar 12-14 ga watan Yunin 2024 duk sun yi wa Ribaɗo magana kan batun. Hakazalika, mista Wray ya gana da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a yayin ziyarar da ya kawo, sai dai Manhaja ba ta gano ko ya tattauna batun Binance da shugaban ƙasa ba.
Wani jami’i daga gwamnatin Amurka ya buƙaci a saki Gambaryan kamar yadda ita ma majalisar dokokin ƙasar a ranar 4 ga watan Yulin 2024 ta buƙaci shugaban ƙasa Joe Biden da sakataren harkokin wajen Amurka da jam’i mai kula da waɗanda aka tsare na fadar shugaban ƙasa, Roger D. Carstens, da su tabbatar da an saki Gambaryan.
Bayan kwanaki bakwai da wancan batu, a ranar 21 ga watan Yuni ne, wasu ‘yan majalisu biyu daga ƙasar Amurka, French Hill and Chrissy Houlahan, suka zo Nijeriya domin domin duba Gambaryan wanda ke tsare a wannan lokaci.
A ranar 10 ga watan Yulin 2024, ‘yan majalisar biyu sun mika rahotonsu kan mista Gambaryan ga majalisar wacce ta buƙaci Nijeriya da ta gaggauta sakinsa tare da kiran Amurka da ta yi amfani da kowanne iko da take da shi domin karɓo Gambaryan.
Har wa yau dai Nijeriya ba ta miƙa wuya ba. A yayin da suke martani ga takwarorinsu na Amurka, Jami’an Nijeriya sun bukaci Amurka da ta girmama Nijeriya a matsayin ƙasa mai ‘yanci da tsarin shari’a. Sannan sun musanta cewa ana tsare da Gambaryan a matsayin mai laifi da ke cikin mawuyacin hali.
“Mista Gambaryan da kamfaninsa suna harkokinsu ne ba tare da samun lasisi ba ko samun izinin, ga kuma ƙin yin biyayya ga dokokin yaƙi da masu safarar haramtattun kuɗi,” a cewar wata takarda da Manhaja ta samu ganinta. Sai dai takardar ta bayyana cewa suna rike da mista Gambaryan ne bisa tanadin doka.
Domin fito da muhimmancin tsare shi, gwamnatin Nijeriya ta bai wa lauyanta umarnin kalubalantar neman beli da mista Gambaryan ya yi a karo na biyu inda mai shari’a, Emeka Nwite, na babbar kotun tarayya da ke Abuja a watan Mayun 2024 ya sake hana Gambaryan beli. Mai shari’a Nwite ya kuma ƙara da cewa Amurka ta gaza gamsar da kotu cewa Nijeriya ba ta da ingantaccen wurin shan magana a gidan yarin da ake tsare da Gambaryan. Daga nan ne kotun ta ɗage zaman shari’ar har zuwa 18 da Octoba da 22-25 ga Nuwamba domin cigaba da sauraron shari’ar.
Wannan ba shi ne abin da Amurka take son ji ba daga zaman shari’ar 11 ga Oktobar 2024 wanda ke nuna yadda Nijeriya ta ƙuduri aniyar tabbatar da doka ta yi aiki a maimakon amincewa da matsayin lambar da suke yi mata. Abin da ya faru a kotu a wannan rana ya tabbatar da cewa Nijeriya da gaske take yi. Daga nan ne Amurka ta yanke shawarar tsage damtse wajen tattaunawa game ta ruwan sanyi.
A rahoto na gaba za ku ji me ya wakana da yadda ƙasashen biyu suka cimma matsaya da ta kai ga jingine ƙarar da ake yi wa Gambaryan da kamfaninsa na Binance wanda ya ba shi damar komawa ƙasarsa ta Amurka.
