
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Shugaban tsohuwar jam’iyyar ANP na ƙasa, kuma Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Rabi’u Musa Kwankwaso a NNPP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Asiwaju Moshood Shittu, ya roƙi jam’iyyun adawa da ke shirin dunƙulewa don kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 da su zaɓi Kwankwaso a matsayin ɗan takara matuƙar suna neman nasara.
Moshood ya yi kiran ne a yayin taron manema labarai, inda ya ce Kwankwaso ne kaɗai wanda ya ke da nagartar da zai iya tunkarar Tinubu a zaɓen 2027 la’akari da gogewarsa a ɓangarori da dama na harkar siyasa da shugabanci.
Don haka ne ya ce, yana ganin dacewar jam’iyyun adawa su ziyarce shi domin yi masa tayin tsayawa takara a babban zaɓen da ke tafe.
Ya ce, sauran ƴan takarar shugaban ƙasa ba su da nagarta da ƙwarewar da za su iya yin galaba akan Shugaba Tinubu, ya na mai bayyana Kwankwaso a matsayin wanda zai iya fafatawa da Shugaban ƙasar na yanzu.
Ya ƙara da cewa, Kwankwaso shi ne wanda ya riƙe muƙamin mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai a lokacin IBB (zamanin mulkin soja) da kuma zama gwamna a 1999.
Haka kuma, ya riƙe muƙamin ministan tsaro da zama jakada na musamman da dai sauransu, don haka ya fi dacewa a ba shi goyon bayan akan sauran.
Kazalika, Moshood ya ya ce da Atiku Abubakar da Peter Obi a matsayin su na manyan ƴan siyasa, ba su da gogewa kamar ta Kwankwaso a fannin siyasa, ya na mai kira a gare su da su mara wa tsohon gwamnan na Kano baya.
