NAPRI za ta kafa cibiyar bincike kan kiwon dabbobi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Cibiyar nazari kan dabbobi ta ƙasa (NAPRI) ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, za ta kafa cibiyar bincike da horar da manoma kan kiwon dabbobi a garin Mahuta da ke ƙaramar hukumar Ƙafur ta Jihar Katsina.

Mataimakin daraktan yaɗa bincike na hukumar NAPRI, Dr. Yunusa Muhammad, ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar cibiyar da suka kai ziyarar aiki ga gwamna Dikko Umar Raɗɗa a gidan gwamnati da ke Katsina.

Dr. Muhammad wanda ya wakilci shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, Farfesa Kabir Bala, ya ce za a kafa cibiyar ne biyo bayan buƙatar haka da al’ummar Mahuta suka gabatar wa cibiyar NAPRI.

Ya bayyana cewa idan aka kafa cibiyar za ta horar da ɗalibai da matasa da mata da masu kiwon dabbobi kan dabarun kiwo na zamani.

Ya ce cibiyar za ta kuma gudanar da bincike da yaɗa ingantattun hanyoyin kiwon dabbobi, da kuma samar da ɓangaren kula da kiwon lafiyar dabbobi da samar da abinci mai gina jiki da yaƙar cututtuka a jikin dabbobi.

Dr. Muhammad ya ce NAPRI za ta buƙaci fili mai faɗin hekta 30 a ƙasar Mahuta domin samar da ciyawa da wajen kiwon dabbobi domin rage rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankin.

“NAPRI za ta yi amfani da wannan fili mai faɗin hecta 30 don bunƙasa kiwo, hakan zai rage dogaro ga filayen gonaki wajen kiwo, kuma zai samar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

“Cibiyar NAPRI da za a buɗe a Mahuta za ta ƙara haɓaka kiwon dabbobi, da inganta lafiyar dabbobi da yaƙi da cututtuka, da bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

“Hakazalika za ta ilmantar da makiyayanmu sabbin tsare-tsaren kiwo na zamani ta hanyar bincike da yaɗa sakamakon binciken don su inganta kiwonsu.

“Samar da babban filin kiwo mai ciyayi iri-iri zai samar wa makiyaya a Mahuta isasshen filin kiwo, ta yadda ba sai sun riƙa kiwo a cikin garuruwan da gonakin mutanen ba”, in ji Dr. Muhammad.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, wanda shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Alhaji Abdulkadir Nasir ya wakilta ya gode wa shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria da cibiyar NAPRI bisa shirin kafaru cibiyar nazari kan kiwon dabbobi a jihar.

Ya ce samar da cibiyar ya dace da shirin gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa na haɓaka harkar noma da kiwo domin samar da wadataccen abinci, da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Ya ce a baya-bayan nan gwamnatin jihar ta raba awaki 40,000 ga makiyaya a faɗin jihar domin bunƙasa harkar kiwo a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar za ta rungumi wannan shirin haɗakar da cibiyar NAPRI tare da bayar da cikakken goyon baya domin a samar da cibiyar bunƙasa kiwo a Mahuta domin inganta rayuwar manoma da kuma kara haɓaka kiwo a jihar.

Alhaji Abdulkadir Nasir ya yi wa tawagar NAPRI alƙawarin mika bukatar su ta haɗin gwiwa ga Gwamna Dikko Umar Raɗɗa, yana Mai basu tabbaci cewa gwamnan na da kishin kawo sauyi a harkar noma da kiwo.

“Al’ummar Mahuta sun rungumi tsarin tabbatar da cigaba a matakin al’uma wanda gwamna Dikko Raɗɗa ya kirkiro, a ƙarƙashin tsarin, kowace al’uma za ta zayyana buƙatunta, sai ta gabatar da su ga gwamnati ta hannun kwamiti a matakin al’umma.

“Ina so in miƙa godiya ta musamman ga Hakimin Mahuta, mai girma Danejin Katsina, da ya jagoranci wannan shiri, Mai girma Gwamna zai yi matuƙar farin ciki da wannan haɗin gwiwa, kuma zai bayar da dukkan goyon bayan da ake buƙata don ganin yayi nasara,” inji Aldulkadir Nasir.

Ya bayyana cewa gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta shiga tsarin kawo sauyi a harkar kiwo da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar.

“Shugaban ƙasa ya samar da ma’aikatar kula da kiwon dabbobi wadda ita ce irinta ta farko a ƙasar nan, kuma yana ba ta dukkanin goyon bayan da take buƙata domin ta bunƙasa harkar kiwo a ƙasar nan.

“A bisa wannan shima mai girma gwamna ya bada matuƙar muhimmanci ga ɓangaren kiwo dabbobi ta hanyar bunƙasa shi da zamanantar da shi don a bunƙasa tattalin arzikin jihar nan”, inji Alhaji Abdulkadir Nasir.

By ukarofi