NGO za ta inganta ɗalibai mata ‘yan sakandare 120 a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna HANS (Hold a Needy and Supports) Centre for Social Justice and Development ta ƙaddamar da wani shirin bada horo na wata uku domin inganta rayuwar ɗalibai mata 120 a Jihar Gombe.

Shirin, wanda aka ƙaddamar da shi a ɗakin taro na Linmana Event Centre, Tunfure, ya haɗa waɗannan matan da ƙwararrun mata daga fannoni daban-daban, kamar likitoci, lauyoyi, injiniyoyi, da sauran ƙwararru.

An tsara shi ne domin zaburar da matan su zama shugabanni da masu tasiri a rayuwa ta hanyar tarukan bita da horo kai-tsaye.

Da take jawabi, Barista Hannatu Dauda Simon, shugabar kwamitin amintattun HANS Centre, ta ce shirin zai ƙarfafa matan wajen samun ilimi da sana’o’i masu tasiri, tare da rage giɓin da ke tsakanin jinsi.

Ta bayyana cewa ɗaliban 120 da aka zaɓo daga mazaɓu 114 na jihar za su samu goyon bayan masu kula don cigaba da basu jagora.

Ta ce: “Manufarmu ita ce gina matan da za su zama masu ƙarfi da ‘yanci, tare da bada gudunmuwa cikin al’umma.”

Shirin na da nufin rage matsalolin cin zarafi da rashin ilimi ga mata, tare da ƙarfafa su wajen zama masu dogaro da kai da kawo canji mai amfani ga al’umma.

By ukarofi