Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon shugaban jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman, ya bayyana komawar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, jam’iyyar SDP da gajen haƙuri.
Lukman ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a a yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa El-Rufai, a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bar APC ya koma SDP tare da bayyana wasu dalilai.
Lukman, wanda abokin siyasar El-Rufai kuma tsohon mamba na kwamitin amintattu na jam’iyyar, ya nuna damuwarsa kan ficewa bagatatan da tsohon gwamnan ya yi wanda ka iya kawo naƙasu ga ƙoƙarin haɗa kan ‘yan jam’iyya da ake shirin yi domin tunkarar zaɓen 2027.
Duk da cewa an yi ta hasashen cewa El-Rufai zai bar jam’iyyar, amma da ya so a ce ƙara haƙuri ya ga yadda tattaunawar za ta kasance.
“Dama ana zaton zai bar jam’iyyar wanda tun a hirar da ya yi a gidan talabijin a kwanakin ya nuna hakan. Sai dai ba wanda ya zaci abin zai zo haka da wuri.”
“Abin da nake zato shi ne zai jinkirta, ya kuma bari mu yi aiki a matsayin ƙungiya a yayin da ke shirye-shiryen fara tattaunawa da ‘ya’yan jam’iyya,” inji Lukman.
Ya ce El-Rufa’i na da ‘yancin shiga kowacce jam’iyya da yake so, sai dai ya nuna fargabar cewa akwai yuwuwar samun matsalar da ba a tunani a komawa wata jam’iyya da ya yi farat ɗaya.
A yayin da yake amsa tambaya kan yuwuwar komawarsa SDP, tsohon darakta janar ɗin ƙungiyar gwamnonin APC ya ce, hakan zai faru ne kawai idan jam’iyyar ta cika sharuɗan da ake buƙata.
“A halin yanzu, ba su cika wannan sharaɗi ba. Muna kan tattaunawa. Idan sun cika sharaɗi a gobe ma, shi kenan,” ya bayyana.
A game da haɗin kan ‘yan siyasa, Lukman ya ce wannan abu ne da ake kan yi.
“Abin tambayar shi ne idan jam’iyyar SDP za ta cika sharuɗan da muke fata.”
Ya ce akwai ‘yan siyasar da burinsu su yi amfani da jam’iyya su samu mulki, amma shi ba ya daga cikin irinsu.
“Abin da ‘yan Nijeriya ke buƙata shi ne jam’iyyar da za ta iya yin gogayya da kowacce iriyar jam’iyya. Idan zan iya tunawa, matsalar ‘yan Nijeriya da jam’iyyar PDP ita ce ƙaƙaba mata ɗan takara.”
