Zan bar Kaduna cikin kyakkyawan yanayi sama da yadda na gaje ta – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alƙawarin barin jihar cikin kyakkyawan yanayi sama da yadda ya same ta, wanda shine dalilin da ya sa gwamnatinsa ke gudanar da muhimman ayyuka kamar na ilimi da lafiya da noma.

Ya ce, wannan ya sa gwamnatinsa ke sake inganta shirye-shiryenta da suka shafi karkara kamar yadda tuni ta fara gudanar da ayyukan gina hanyoyi guda 78 a faɗin jihar Kaduna tun bayan zamansa gwamnan Kaduna.

Gwamnna ya jaddada cewa waɗancan ayyuka na tafiya yadda suka dace a yayin da tuni aka bai wa ‘yan kwangilar isasshen kuɗi domin tabbatar da cewa sun kammala aiki a cikin wa’adin da aka ɗiba. Wannan dai ya ce yunkuri ne ganin an haɗa al’ummar karakara da birane saboda inganta tattalin arziƙinsu.

Ya tabbatar da himmatuwa wajen gudanar da ayyukan hanyoyi a cikin garin Zaria daga mahaɗar Magajiya Junction zuwa Kasuwan Amaru da haɗe titin Unguwan Liman/Albarkawa da titin Audi zuwa Kako a ƙaramar hukumar Zariya.

“Idan aka kammala aikin hanya ta ganrin Zariya, za ta taimaka wa al’umma da dama da musamman talakawan da ke zaune a garin. Samar da ayyukan yi da inganta ayyukan kasuwanci da tsaro cikin gari da kewaye,” ya bayyana.

A cewarsa, Zariya tafi gaban a bar ta a irin halin da ya same ta, yana mai cewa, “wannan yunƙuri ne da zai tabbatar da cewa an samar da hanyoyi da faɗaɗawa da gyara wadanda ake da su domin sauƙaƙa zirga-zirga da kasuwanci a faɗin jihar.

“Wannan hanya daga Audi zuwa Kako wanda ke wajen Zariya zai haɗa manona da al’ummar da ke noma. Gwamnatinmu ta himmatu wajen bunƙasa cigaba ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa a dukkan ƙananan hukumominmu da tallafa wa al’ummomi domin samun cigaba da sauri da cike giɓin da ake akwai na ayyukan raya ƙasa da magance kwararar ‘yan ƙauye zuwa birni da inganta tsarin rayuwar al’ummomin.”

A yayin da yake magana tun da fari, shugaban ƙaramar hukumar Zariya, Engr. Jamil Ahmad, ya gode wa gwamnan kan irin ayyukan raya jihar da yake aiwatarwa.

Shugaban ya yi wa gwamnan alƙawarin samun goyon bayan mutanen Zariya da alƙawarin zai samu ƙarin ƙuri’a kan wacce suka ba shi a babban zaɓe mai zuwa (2027).

Shi ma a nasa jawabin, sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi wa gwamna, Uba Sani home, barka da zuwa gida yana mai cewa gwamnan ɗan gida ne a garin Zariya.

Sarkin wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan Kaduna, ya kuma yaba wa gwamnan kan irin ayyukan cigaba da yake yi a faɗin jihar.

By ukarofi