Manyan makarantun Kano sun sami ƙarin albashi

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ƙarin albashi tsakanin kashi 25 zuwa 35 ga ma’aikatan manyan makarantun jihar, ciki har da ma’aikatan ilimi. Kwamishinan yaɗa labarai, Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Kano, inda ya ce ƙarin zai fara aiki daga watan Maris 2025. Ya bayyana cewa malaman makarantu za su samu ƙarin albashi na kashi 25, yayin da ma’aikatan da ba na koyarwa ba za su samu kashi 35. Wannan matakin an ɗauke shi ne a zaman majalisar zartarwa ta jiha domin ƙara inganta walwalar ma’aikata da kuma ƙarfafa harkar ilimi a ƙarƙashin manufofin gwamnati na dokar ta-ɓaci kan ilimi.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta amince da kashe naira biliyan 3.4 domin aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a faɗin jihar. Daga cikin ayyukan akwai naira miliyan 612.4 da aka ware domin sauya tsarin wutar lantarki daga na sama zuwa na karkashin kasa a fadar gwamnati da kuma kwashe layukan wuta a titin Ahmadu Bello Way. Haka kuma, an ware naira miliyan 148.9 domin gyaran hanyoyin makarantar kimiyya ta Kano (School of Technology) ƙarƙashin hukumar gyaran hanyoyi ta Jihar Kano (KARMA).

Sauran muhimman ayyuka sun haɗa da naira miliyan 367.9 da aka fitar a matsayin kuɗin fara faɗaɗa titin Zaria daga Silver Jubilee zuwa Ɗantata & Sawoe. Haka kuma, an ware naira miliyan 184 domin sayen motocin asibiti guda biyu ga asibitin fadar gwamnati da asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli. Gwamnati ta kuma bayar da naira miliyan 348 domin biyan kuɗin wuta ga KEDCO na watannin Nuwamba da Disamba na shekarar 2024. Bugu da ƙari, an fitar da naira miliyan 662 domin ciyar da ɗalibai a makarantun kwana daga mako na uku zuwa na biyar na zangon karatu na yanzu. Haka kuma, gwamnatin ta amince da naira miliyan 100 domin tallafawa ƙungiyar tsoffin ma’aikata (Nigeria Union of Pensioners) wajen gudanar da taron wakilai na kowane shekaru huɗu a Kano.

By ukarofi