Nnamdi Kanu ya nemi afuwa bisa zagin alƙalai

Spread the love

Shugaban ƙungiyar da aka haramta ta IPOB, Nnamdi Kanu, ya nemi afuwa bisa zagin da ya yi wa Kotun Tarayya da Mai Shari’a Binta Nyako. Kanu ya gabatar da wannan afuwa ne ta hannun sabon lauyansa kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya da Ministan Shari’a, Cif Kanu Agabi (SAN), yayin zaman kotu a gaban Mai Shari’a James Omotosho.

Cif Agabi, wanda ya jagoranci tawagar lauyoyin Kanu, ya kuma nemi afuwa ga lauyan Gwamnatin Tarayya, Cif Awomolo (SAN), da kuma tawagar lauyoyin Kanu na baya ƙarƙashin jagorancin Aloy Ejimakor, bisa zagin da Kanu ya yi musu a gaban Mai Shari’a Nyako. Ya bayyana cewa an riga an tattauna da lauyan masu gabatar da ƙara kan wannan ci gaban, kuma kotu ta amince da gabatar da saƙon afuwar.

Tun bayan da aka dawo da Kanu daga Kenya a watan Yuni 2021, ana ci gaba da fafatawa kan batun tuhumarsa bisa zargin ta’addanci. An fara shari’ar ne a gaban Mai Shari’a Binta Nyako, amma daga baya aka sauya alƙalin zuwa Mai Shari’a James Omotosho, bayan Mai Shari’a Nyako ta janye daga shari’ar bisa rashin amincewa da ita daga ɓangaren Kanu. A halin yanzu, ana sa ran Kanu zai bayyana a gaban kotu domin ɗaukar mataki na gaba kan tuhumar da ake masa.

By ukarofi