Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Gamayyar ƙungiyoyin addinin Musulunci na Jihar Sakkwato tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Asshafi’i da wasu ƙungiyoyi masa tallafawa harkokin addinin Musulunci, sun shirya wata gagarumar liyafa don tarbar wata baiwar Allah mai suna Maryam Musa, wacce ta bijire wa mijinta da ya nemi mayar da ita da sauran iyalinsa zuwa addinin Kirista.
Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne wani bidiyo ya yi yawo a zaurukan sada zumunta game da wani ɗan Jihar Sakkwato mai suna Alhaji Musa Tsamaye daga ƙaramar Hukumar Mulki ta Sabon Birni ya kwashi iyalansa sun 13 daga Sakkwato zuwa Jihar Taraba domin canja musu addini daga Musulunci zuwa Kiristanci. Maryam na daga cikin matansa da ta bijire ta ƙi yin biyayya ta jajirce kan imanin ta da addinin Musulunci.
Bayan doguwar muhawara da kai ruwa rana, ita dai Maryam ta samu komawa Sakkwato, ƙarƙashin jagorancin haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci, waɗanda ke samun jagorancin shugaban Majalisar ƙungiyoyin Musulunci masu aikin Da’awa ta ƙasa (DCCN) kuma Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki da Sheikh Musa Assudani.
A sakamakon haka ne reshen ƙungiyoyin da ke Jihar Sakkwato suka shirya liyafa ta musamman don nuna ’yan uwantaka da yabawa da dagewar Maryam kan imanin ta. Daga cikin mahalarta taron akwai malamai, mata, matasa, ɗalibai da ma’aikatan lafiya Musulmi, da sauransu.
Tun daga farko sai da aka yi mata gagarumin tarba a filin jirgin saman Sarkin Musulmi Muhammadu Abubakar na uku da ke Sakkwato, tare da shirya tattaunawa ta musamman a cibiyar yaɗa addinin Musulunci ta IET, tsakanin shugabanni da mambobin ƙungiyoyin.
Shugaban Cibiyar na ƙasa, Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato, da Shugaban Gidauniyar Imamu Shafi’i Sheikh Musa Assudani, sun bayyana cewa an shirya wannan tarbar ne domin nuna so da ƙauna ga Maryam. Sun kuma kiraye ta da ta yi riƙo da kyawawan ɗabi’un Musulunci, da suka haɗa da so da ƙaunar juna, samar da zaman lafiya da aminci, kariya da mutunta juna.
Yayin da wasu shugabannin ƙungiyoyin suka nuna jin daɗinsu ga wannan talikar da kuma bata tabbacin tafiya tare da ita, don gudanar da harkokin yaɗa addinin Musulunci. Sun kuma ƙara bata shawarar da ta dage cikin addinin Musulunci, tare da karramata da wasu kyaututtuka da suka haɗa da sutura, kuɗaɗe da dai sauransu.
A nata ɓangaren, Maryam Musa ta yi godiya kan ‘yan uwantakar addinin Musulunci da aka nuna mata, tare da bayyana yaƙinin cewa, addinin Musulunci shi ne karɓaɓɓen addini a wajen Allah. Don haka babu wanda zai canza mata fahimta.
