Gwamnan Filato ya yi jimamin rasuwar fitaccen jarumi, Karƙuzu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya bayyana alhininsa game da rashin fitaccen jarumin finafinan Hausa, Abdu Kano da aka fi sani da Karƙuzu, wanda ya rasu bayan fama da wani rashin lafiya.

A saƙon ta’aziyyarsa da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan yaɗa Labaransa, Gyang Bere, gwmanan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hikima wanda mutuwarsa ta haifar da babban giɓi ga iyalansa da masana’antar finafinai da jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya ce, Karƙuzu ya bada gagarumar gudummawa a harkokin finafinan Hausa ta hanyar amfani da shirye-shiryensa wajen ilmantar da al’umma, nishaɗantar da su da kuma wayar masu da kai game da muhimman abubuwan zamantakewa.

Haka kuma, ya ce Karƙuzu sadaukarwarsa ba ga iya al’ummar Filato ta tsaya ba, aba ce da ta kewaye Arewacin Nijeriya, lamarin da ya sa ya zama abin kwaikwayo ga al’umma.

A madadin gwamnatin Filato da al’ummar jihar, ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, ya na mai masu fatan samun juriya da dangana a yayin jimamin babban rashin da aka yi masu.

By Babaji