Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An shiga fargaba yayin da ‘yan sandan Nijeriya a halin yanzu ke gudanar da bincike kan wani batu na kutsen KGB na Rasha, wata ƙungiyar da ake kira ‘Komitet Gosudarstɓennoy Bezopasnosti’, tsohuwar hukumar leƙen asiri ta Tarayyar Soɓiet a Majalisar Dokokin Nijeriya.
Hedikwatar ‘yan sandan ta gayyaci Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sunday Karimi, domin amsa tambayoyi biyo bayan koken da takwararsa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan hakan, kamar yadda aka gano.
A cewar ƙorafin mai ɗauke da kwanan watan 5 ga Maris, Sanata Akpoti-Uduaghan, wacce a halin yanzu ta ke zaman dakatarwa daga majalisar na tsawon watanni shida, ta buƙaci ’yan sanda su binciki iƙirarin da takwaranta daga Kogi ta Yamma ya yi cewa, KGB ta kutsa cikin majalisar dokokin ƙasar, wanda hakan ke kawo babbar barazana ga tsarin dimukraɗiyyar ƙasar.
Sanata Akpoti-Uduaghan, a cikin ƙarar, ta yi zargin cewa Sanata Karimi ya raba wani rahoto mai taken: “Wakilin KGB ya gargaɗi Majalisar Dattawa: Kiran taka-tsan-tsan a cikin barazana ga dimukraɗiyya” a rukunin WhatsApp na Majalisar Dattawa ta 10 a ranar 23 ga Fabrairu.
A cikin ƙarar da ta shigar, ‘yar majalisar ta Kogi ta tsakiya ta buƙaci ‘yan sandan da kada su yi la’akari da furucin da Sanata Karimi ya yi, inda ta ce, “Babu wata ƙasa da za ta iya yin watsi da kasancewar irin wannan ƙungiya a cikin majalisarta.”
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa Sanata Karimi ya bayyana a Louis Edet, hedkwatar ‘yan sanda a ranar Litinin ɗin makon nan inda aka yi masa tambayoyi game da koken bayan gayyatar ‘yan sanda.
Majiyoyi a hedikwatar ‘yan sandan sun ce Karimi ya mallaki muƙamin a dandalin WhatsApp na majalisar dattawa ta 10 yana mai cewa ba shi da wata illa.
