
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar 29 ga watan Maris ne za a yi addu’o’i na musamman a babban Masallacin Ƙasa na Abuja, a yayin da Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke cika shekaru 73 a duniya.
Kakakinsa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a ranar Alhamis cikin wata takarda, inda ya ce Shugaban zai kuma yi amfani da damar hakan wajen gode wa Allah SWT da Ya yi riƙo da hannunsa wajen jagorancin al’ummar Nijeriya.
Lamarin da ya dace da watan Ramadana kuma watanni biyu gabannin cikarsa shekaru biyu akan karagar mulki.
Za kuma a yi addu’o’i ga ƙasa domin cigaba da samun nasarori, zaman lafiya da kwanciyar hankali acikin al’ummar Nijeriya.
Onanuga ya ce, hakan ya nuna yadda Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin jajircewa wajen samar wa Nijeriya nasarori a kowane ɓangare da taimakon Allah SWT da samar da zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Ya kuma ce, Shugaban ƙasar ya yi kira ga ɗaukacin al’umma su gudanar da addu’a makamanciyar wadda za a yi a masallatansu don ƙarfafa ta a yayin neman dacewa da rahamar Allah SWT.
