EFCC na neman Aisha Achimugu ruwa a jallo

Spread the love

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana shahararriyar ‘yar kasuwa, Aisha Achimugu, a matsayin wacce ake nema ruwa a jallo kan zargin haɗa kai wajen aikata zamba da halasta kuɗin haram.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya fitar da wata sanarwa a shafinsu na X a ranar Juma’a, yana kira ga jama’a da su taimaka da bayanai kan inda take.

Sanarwar ta ce, “Ana sanar da jama’a cewa Aisha Sulaiman Achimugu, ‘yar asalin karamar hukumar Ofu a Jihar Kogi, tana fuskantar bincike kan zargin haɗa baki wajen aikata zamba da halatta kuɗin haram. An bayyana adireshinta na ƙarshe da aka sani a matsayin 6C, Rudolf Close, Maitama, Abuja.”

EFCC ta buƙaci duk wanda ke da wani muhimmiyar bayani game da inda take da ya tuntubi ofisoshinta a Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, ko Abuja. Hakanan, ana iya tuntuɓar hukumar ta wayar salula a lamba 08093322644 ko ta adireshin imel ɗinsu: [email protected], ko kuma a kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

By ukarofi