DAGA JOHN D. WADA a Lafiya
Babban sakataren hukumar kiwon lafiya a matakin farko wato Nasarawa State Primary Health Care Development Agency a turance ta gwamnatin Jihar Nasarawa Dakta Usman Iskilu Saleh yace kawo yanzu gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule yana cigaba da bada fifiko da tallafi na musamman ga fannin kiwon lafiya a jihar musamman a matakin farko.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilan mu a ofishin sa dake hukumar a Lafiya babban birnin jihar.
Dakta Usman Iskilu Saleh yace a matsayin sa na wanda yayi aiki da gwamnan ya kuma kasance likitan sa sama da shekaru 4 har zuwa matsayin sa na yanzu yana da cikakken masaniyar ire-iren ɗinbin gudumawa da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule din ke bai wa fannin kawo yanzu.
Ya ƙara da cewa gwamnan yana yin haka ne ta ingataccen tsare-tsaren gwamnatin sa na musamman da samar da magunguna da kayayyakin kiwon lafiyar irin na zamani a duka matakai musamman a matakin farko ta kiwon lafiyar da sauran su baya ga turo tallafin kuɗaɗe zuwa ga hukumomin lafiyar daban daban da naɗa ƙwararru a fannin a kowanne lokaci da sauran su.
Dangane da ire-iren ayyukan hukumar nasa na kiwon lafiya a matakin farko, babban sakataren Dakta Usman Iskilu Saleh ya bayyana cewa hukumar kamar sauran takwarorin sa dake faɗin ƙasar nan suna aiwatar da shirye-shirye da tsare-tsaren hukumar kiwon lafiya ta duniya ce tare da haɗin gwiwar babban bankin duniya da sauran abokan hulɗa don amfanar al’umma musamman waɗanda ke yankunan karkara inda ya ƙara da cewa tuni gwamnatin jihar ta hukumar ta kuma fara aiwatar da wani shiri na musamman don sabunta tare da farfaɗo da duka asibitoti da ƙananan asibitocin je ka-da iyalan ka dake duka gundumomi 147 na jihar don tabbatar suna aiki dare da rana kafin ƙarshen watan Yuni da sauran su.
Da yake jawabi har ila yau game da nasarori da hukumar ta cimma a kulawar sa cikin lokaci ƙalilan da yayi a kujera a matsayin babban hukumar kiwon kafiyar mai matukar mahimmanci Dakta Usman Iskilu Saleh yace a yanzu haka ma’aikatan hukumar kiwon lafiyar suna zuwa aiki cikin lokaci sakamakon zama da yake yi dasu akai-akai yana jaddada musu mahimmancin yin haka tare da nuna musu misalin haka a zahirance inda suke yin koyi da shi da sauran nasarorin.
A ƙarshe sai yayi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga al’ummar jihar baki ɗaya dama waɗanda ke yankunan karkara su cigaba da bai wa hukumar cikakken goyon baya musamman ta kula da kaddarorin gwamnati musamman na kiwon lafiyar dake yankunan su don su daɗe suna amfana da su kana ya sha alwashin cigaba da gudanar da shugabanci nagari a hukumar don amfanar al’ummar jihar dama ƙasa baki ɗaya.
