Abokin karawar fitaccen ɗan wasan damben boksin na duniya Muhammad Ali, Gorge Foreman ya rasu.
A 1974 George Foreman ya sha lallasa a karawarsa da Mohamed Ali a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Wasan da aka yi wa take da ‘Wasan ƙarni’ tsakanin manyan ‘yan wasan damben duniya biyu dukan su daga Amurka, sama da mutum dubu 100 ne suka kalle shi kai tsaye
Sau biyu Foreman ke lashe kambun duniya a gasar ta dambe kafin ya faɗi a hannun Mohamed Ali.
An haifi George Foreman a wata unguwa ta baƙar fata marasa galihu a Houston na Amurka.
A cikin wata sanarwa da iyalansa suka wallafa a shafukan sada zumunta, sun bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki mai tausayi wanda ake girmamawa sosai.
