
Daga BELLO A. BABAJI
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da ikirarin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na cewa Hukumar EFCC ta shirya gudanar da bincike akan sa.
A ranar Juma’a ne Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a wata takarda , inda ya ce batun ƙarya ne wanda aka ƙirƙiro da nufin tada yamutsi a kafafen sadarwa.
A ranar Alhamis ne Atiku ya ce EFCC ta yi bincike akan sa kan cewa ya na da hannu a almundahanar wasu kuɗaɗe da aka alaƙanta da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Onanuga ya ce, lallai an watsa batun ne da nufin haddasa cecekuce acikin al’umma da sunan siyasa, ya na mai cewa darajar Atiku ta wuce a riƙa amfani da ita waje yaɗa batutuwa mara asali.
Ya kuma ce, Shugaba Bola Tinubu ba shi da lokacin tsoma baki game da batutuwan da suka shafi munafurci, yayin da ya mayar da hankali wajen warware matsalolin da ƙasa ta ke fuskanta.
Haka kuma, ya yi kira ga Atiku da ya sauya aƙalar masa wajen ƙoƙarin samar da haɗin kan ƙasa da abubuwan na bunƙasa ƙasa da Nijeriya ke buƙata wajen ciyar da ita gaba.
