
Daga BELLO A. BABAJI
Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya damƙa mutane 19 da aka yi garkuwa da su ga Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa don ya miƙa su ga iyalansu.
Jami’an sojoji da na wasu hukumomin ne suka ceto su daga sassa daban-daban na ƙasar bayan gudanar atisaye a yayin ayyukansu.
Daga cikin waɗanda aka damƙa wa CDS ɗin akwai tsohon Darakta-Janar na Hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) da Ambasada Gideon Yohanna.
A ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi garkuwa da Tsiga a ƙauyensu na Tsiga dake Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.
