Filato: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Ɓokkos

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne wasu ƴan bindiga suka farmaki mutane a ƙauyuka biyar na Ƙaramar Hukumar Ɓokkos dake Jihar Filato, inda suka kashe kimanin mutane 10.

Shugaban Majalisar Ci-gaban Al’adun Ɓokkos (BCDC), Farmasun Fuddang da Sakatarenta, Ambasada Duwam Bosco suka bayyana hakan a wata sanarwar haɗaka, ranar Alhamis.

Sun ce, a cikin sati guda sun rasa mutane aƙalla 20 daga masu faɗan addini da ƙabilanci a ƙauyuka biyar dake ƙaramar hukumar, inda a ranar 2 ga watan Afrilu kaɗai mutane 10 aka kashe.

Majalisar ta kuma ce, maharan sun fara ne da kai farmaki da tsakar rana a ƙauyen Mangor Tamisu, sannan sai suka garzaya Daffo da Manguna, kana daga bisani suka je Hurti da Tadai.

Daga nan ne jami’an soji suka gaggauta kai ɗauki sakamakon kiraye-kiyare, inda suka taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addancin.

Bugu da ƙari, majalisar ta yi kira ga ɗaukacin al’ummar ƙaramar hukumar da su ɗauki matakin kare kawunansu, kamar yadda Gwamna Caleb Mutfwang ya bada shawara a baya.

Saidai, ba a samu wani jawabi daga rundunar ƴan sandan jihar ba, duk da ƙoƙarin neman su da aka yi, domin ji ta bakinsu game da lamarin a yayin haɗa rahoton.

By Babaji