IMF ta nemi Tinubu ya kyautata rayuwar talakawan Nijeriya 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Nijeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni.

Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C.

Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Nijeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi.

Manhaja ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa sama da Naira 1,000.

Wannan sauyi ya jefa ’yan Nijeriya da dama cikin matsananciyar wahala.

Duk da haka, Kozack ta amince da ƙalubalen da jama’a ke fuskanta kuma ta jaddada buƙatar tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.

Ta buƙaci gwamnati da ta mayar da hankali kan shirye-shiryen jin daɗin al’umma, kamar bayar da tallafin kuɗi, tare da inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.

Haka kuma, ta sanar da cewa jami’an IMF za su ziyarci Nijeriya nan ba da daɗewa ba domin nazarin manufofin tattalin arziƙi na shekarar 2025 a ƙarƙashin shirin bincike na ‘Article Iɓ’, wanda ke tantance yanayin tattalin arziƙin ƙasashe mambobin IMF.

By ukarofi