Yadda farashin fetur zai ƙaru sakamakon hana saida ɗanyen mai a Naira

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHANMAD

Sabon tsarin sayar da man fetur a Nijeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa.

A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira.

Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Rahotanni sun nuna cewa farashin ya fi ƙaruwa a Arewa, yayin da Legas ke da mafi ƙarancin farashi.

Kamfanin mai da gas na MRS na jigilar mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na ƙasar.

Duk da haka, ba a bayyana takamaiman wajen da aka sayo sabon man fetur ba, amma yanzu ana sayar da shi a farashin da ya bambanta da na baya.

A halin da ake ciki, hana wani sauyi a minti na karshe, ana sa ran matatar mai ta Dangote ta rufe ganga 650,000 a kowace rana don rufe sashin da take hako mai domin kula da shi. A cewar Reuters, kulawar, wanda zai iya faruwa a watan Yuni, zai ɗauki kwanaki 30.

Dangane da batun cinikin danyen mai na Naira, wani mai bincike a ma’aikatar kuɗi da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi ya bayyana cewa ba a samu wani gagarumin ci gaba ba. Majiyar ta ce dukkan bangarorin biyu ba za su iya shiga wani taro ba a cikin makon da ya gabata.

“Babu wani sabon abu da ya faru. Wataƙila bayan hutu, kwamitin zai zauna ya gana,” inji babban jami’in gwamnatin.

Za a iya tuna cewa, a ranar 1 ga Oktoba, 2024, gwamnati ta fara siyar da danyen mai a naira ga matatar Dangote domin inganta samar da man fetur, da ceton ƙasar nan na miliyoyin daloli da ake shigo da man fetur daga ƙasashen waje, sannan a karshe an rage farashin man fetur.

A kwanakin baya kamfanin mai na ƙasa NNPC ya bayyana cewa matatar man Dangote ta samu gangar ɗanyen mai miliyan 48 a naira ƙarƙashin yarjejeniyar. Haka kuma ta ce an kawo jimillar danyen mai miliyan 84 ga matatar tun da ta fara aiki a shekarar 2023.

Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa yarjejeniyar farko ta kasance na tsawon watanni shida kuma ana ci gaba da tattaunawa kan sabunta yarjejeniyar, da nufin kafa sabuwar kwangila.

Sai dai al’amura sun dagule sosai a lokacin da matatar man Dangote a ranar 19 ga watan Maris ta sanar da dakatar da sayar da man fetur na wucin gadi a naira.

Matatar mai da ke Lekki ta koka da yadda aka samu rashin daidaito tsakanin kuɗaɗen da ake sayar da ita da kuma wajibcin sayan ɗanyen mai da ta ce a halin yanzu ana sayar da shi a kan dalar Amurka.

By ukarofi