Mafi yawan mutuwar aure laifin mata ne – Hussaina Shafi’u

Spread the love

“Na san wahalar da mata marasa miji suke fuskanta”

“Sana’ar mafifi ce sana’ar da na dogara da ita”

Daga UMAR AKILU MAJERI 

Hussaina tana ɗaya daga cikin matasan mata a yankin ƙaramar Hukumar Kiyawa da ta yi fice wajan yin saƙa musamman saƙar mafici wadda ake yin amfani da shi wajan yin fifita a gidajan masu hannu da shuni.

Hajiya Hussaina ba ta tsaya iyanan ba malama ce da take da ilimin addini, ga haƙuri, ga kuma sanin darajar mutane. Ba ta da saurin fushi ga karamci wajan girmama al’umma.

Wakilinmu na Jihar Jigawa Umar Akilu Majeri shi ne wanda ya samu ikon ganawa da ita Hajiya Hussaina a falon gidanta na aure, inda tattaunawar ta karkata kan yadda sana’ar yin mafificin roba ta ɗaukaka ta a duniya.  

Hajia Hussaina wadda akafi sani da maman safuwan ta bayyana cewar Tasha wahala awajan Mijinta na fari kasancewar tanada haƙuri bata san wani abu wai shi kishi ba kamar yadda matan hausawa suke wa maza ba. Ta ce irin kishinnan na ci wa mazaje mutunci bata yinsa domin shi ne yake taimaka wa wajan mutuwar aure. 

Ta ce, hakan ne ya bai wa tsohon mijinta na baya damar yi mata wulaƙanci kala-kala har takai ga yi mata sakin wulaƙanci bayan suna da ‘ya’ya uku dukkansu maza. Ta ce haka ya sa ta ji gabaɗaya ta tsani rayuwar aure abaya domin gani take dukkan mazaje haka suke.

Kada in cika ku da surutu, ga dai yadda ta kasance a firar tasu;

MANHAJA: Ko za mu iya jin ko wacce ce baƙuwar tamu?

HAJIYA HUSSAINA: Sunana Hajiya Hussaina Shafi’u, Maman Safiyan, wadda ayanzu na koma Maman Zara ake cemin, ko Hussaina Umar mai mafici.

Me ya sa ake ce maki mai mafici ?

Saboda sana’ata ce, ita na iya, kuma ita nake yi. Kuma alhamdulilla, tana rufa min asiri daidai gwargwado, domin da wannan sana’ar bayan rabuwa ta da tsohon mijina na samu cigaba a rayuwata.

Mutane zasu yi mamakin ki ace mace kamarki ta dogara da saƙar mafici?

Meye abin mamaki a ciki, bayan na sanu nasibi a wannan harka, domin na yi wa kowa fintinkau saboda sana’ata ta manyan mutane ce, sarakuna, da kuma manyan ma’aikata da ma’aikatan banki, ta kai har bukkin suke yi na mafici na. Ma’ana dai yana ƙare wa ne a hannu, ba tare da na ɗauka, na yi talla ba.

Ko yanzu da nai aure, mijina yake ɗauka ya kai wa waɗanda suka saya domin lambar wayarsa nake amfani da ita wajan harkokin kasuwancina. A halin yanzu na sauke latina da aka danni dashi domin shi ne mijina, shi ne ya kamata ya taimakamin kuma yana yi min saboda ba shi da ƙyashi ko mugunta.

Kina yin saiti nawa a wata?

Na kan yi saiti goma sha huɗu hudu na mafici a duk sati 4, na kan yi saiti goma sha 16 a wata kuma duk saiti nakan sayar da shi akan Naira dubu biyu da ɗari biyar, kaga wata ina samun aƙallah dubu talatin da takwas.

Kuma nawa kike kashewa wajan sayan kayan aiki ?

Nakan kashe dubu takwas a wata wajan siyan kayan aiki.

Kamar dame-dame kike yin amfani da shi wajan wannan sana’a taki?

Ina sayan ɗaurin robar tabarma, duwatsun ado, da tamkar dabino da sayar yankawa. Ita sana’ar mafici bata buƙatar wani dogon jari wadda zai fara yana iya fara wa da jarin dubu gomasha biyar, amma kamar ni a yanzu ina da jarin da ya kai Naira dubu ɗari biyu. Ina da masu logo aƙasa na kamar mutun talatin.

Suwaye suka fi amfani da maficinki?

Waɗanda suka fi sayan maficina su ne ma’aikatan banki da sarakuna da manyan Yan kasuwa saboda na kan yi mai ado da gashin ɗawisu ko gashin jimina wadda sarakuna ne kawai suke saya, ni ma kuma bana sayarwa kowa sai su.

Tsawon shekara nawa kuka yi kina wannan sana’ar?

Tsawon shekara huɗu ina yin wannan sana’a, kuma tayi min duk abinda nake da buƙata.

A ganinki me ya sa aure yake yawan mutuwa?

Magana ta gaskiya laifin mata ne, mafiya yawancin mata suna gabatar da ƙorafi ga mazaje ba sa barin namiji ya nutsu idan ya dawo gida daga wajan aiki ko kasuwa, hakan ya sa wasu mazajen suke sakin matayensu lamarin da ya sa mafiya yawan mazaje basa iya yin haƙuri suke sakin matan.

To kenan ke ma kina cikin irinsu?

A’a ai ni nawa daban yake wallahi, ni ban taɓa yin sa’insa da mijina ba, ya sake ni ne saboda yana san yin aure da rauni musamman mata da aka ce zawarawa ne akwai buƙatar naga na taimaka masu, domin na san wahalar da mata marasa miji suke fuskanta, domin ni ma na yi zama a mazauninsu. Na yi irin wannan zaman, na ji yadda ake ji .

Menene saƙonki ga masu buƙatar mafici da mata masu son koyan sana’ar mafici?

Ina son na gaya wa masu buƙatar mafici da su riƙa tuntuɓar mijina, shi ne shugabana. Su kuma masu san koyan maficin ƙofa a buɗe take a shirye nake na koya masu don Inga na inganta rayuwarsu. 

Na gode Hajiya.

Ni ma na gode.

By ukarofi