Wata mota ƙirar Toyota Hiace mai kujeru 18 ɗauke da lambar rajista KTG 283 XA ta afka cikin kasuwar Damagum da ke jihar Yobe, inda ta hallaka wata mai juna biyu tare da wasu mutane huɗu. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, yayin da mutane ke shirin tashi daga kasuwa.
Shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Yobe, Livinus Yilzoom, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutane 19 sun jikkata, yayinda mutanen da suka mutu ba fasinjojin motar ba ne, sai dai mutane ne da ke gefen hanya suna ƙoƙarin ƙetare titi lokacin da direban ya gaza riƙe motar.
Yilzoom ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa gudun wuce sa’a da rashin iya sarrafa motar ne suka haddasa mummunan haɗarin. Ya ce jami’ansu daga ofishin Dogon Kuka sun hanzarta zuwa wurin da haɗarin ya faru domin ceto waɗanda suka jikkata tare da kai su asibitin Damagum domin samun kulawa.
A wani lamari makamancin haka, rahotanni sun bayyana cewa wasu masu wa’azi huɗu sun rasa rayukansu a wani haɗarin mota da ya faru a kan hanyar Ikorodu-Sagamu a Jihar Ogun. Masu wa’azin sun haɗa da Evangelist Ayodeji David (Kekere Jesu), Evangelist Iyanu Joseph, Opeyemi Adesina da Monjolajesu Oluwapamilerin. Hukumar FRSC ta ce sun rasu ne bayan motar da suke ciki ta yi taho mu gama da wata mota sakamakon gudun wuce sa’a da kuma rashin kyawun gani a hanya.
