Shettima ya bada umarnin magance yawan lalacewar rumbun lantarki na ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya umarci mambobin Ƙungiyar Daraktocin Kamfanonin Lantarki (NISO) da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukansu don tabbatar da samun wadataccen wutar lantarki a Nijeriya.

Ya ce, yayin da suka jajirce wajen aiki kafaɗa-da-kafaɗa, hakan zai taimaka wajen cimma manufar gwamantin Shugaba Tinubu na warware matsalolin da fannin lantarki ya ke fama da shi a ƙasar.

A yayin da ya ke magana a taron ƙaddamar da kwamitin Amintattu na NISO a Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Talata, Shettima ya ce Gwamantin Tarayya ta mayar da hankali wajen tabbatar da gaskiya da adalci a fannoni da dama, ya na mai kira a gare su da su yi amfani da damar ƙwarewarsu wajen kawo gyara a fannin don samun wadataccen lantarki mai ɗorewa a ƙasar.

Ya Kuma ce, amincewa da kafa kwamitin amintattun da Shugaba Tinubu ya yi, ya dace da sashe na 30(2) na dokar ƙasa wanda ke magana akan naɗa ƙwararru kuma jajirtattun ma’aikata a fannin da ya dace da su.

Ya ƙara da cewa, nan gaba Babban Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN, zai miƙa baki ɗaya abinda ya mallaka da ke da alaƙa da kasuwanci da gudanarwa ga NISO, kamar yadda sashe na 15(2) na dokar ƙasa ya bayyana.

Kazalika, Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsu wajen gyarawa da inganta masana’antar raba wutar lantarki ta Nijeriya (NESI), kamar yadda mataimaki na musamman kan yaɗa labarai ga shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda.

By Babaji