Hon. Ɗanbaba ya taya Kwamared Salihu Ɗantata murnar zama mataimaki na musamman ga Minista Goronyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɗan majalisar dokoki da ke wakiltar mazaɓar Kaiama/Kamanji/Wajibe a Jihar Kwara, Hon. Abdullahi Halidu Ɗanbaba, ya taya Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud bisa samun muƙamin mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Ƙaramin Ministan Ayyuka, Muhammad Bello Goronyo.

Ya ce, Kwamared Salihu Ɗantata aboki ne na ƙwarai kuma ɗan yankin Kaiama, wanda ya bada gudunmawa sosai wajen ci-gaban al’umma a yankinsa.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, Hon. Ɗanbaba ya bayyana cewa, naɗin Ɗantata ya biyo bayan ƙwarewarsa ne da ƙoƙarin bada gudunmawa ga ci-gaban ƙasa.

Ya kuma bayyana farin cikinsa game da al’amarin, ya na mai kira a gare shi da ya cigaba da kare martabarsa a idon al’umma wajen jajircewa da tsayuwa akan daidai a yayin sauke nauyin da aka ɗora masa.

Kazalika, ya tabbatar masa da cewa zai bada duk wata gudunmawa da ake buƙata wajen ganin ya yi nasara a yayin gudanar da ayyukansa, wanda hakan abin alfahari ne a gare shi da al’ummar mazaɓarsu.

By Babaji