Arewa maso Yamma: Gamayyar ƙungiyoyi sun yaba wa Tinubu da Matawalle bisa ingancin tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da ke da wakilci a ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya ta yi godiya da jinjina ga Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Ministan ƙasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Dr Bello Matawalle, da babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa, bisa haɗa hannu wajen inganta tsaro a yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi a birnin Abuja, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Dr Usman Goronyo, ya danganta raguwar ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da shugabanci na gari, kwarewa da hangen nesa na Minista Bello Matawalle, tare da babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa, da Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

Musamman ƙungiyar ta jaddada muhimmancin umarnin da Matawalle ya bayar a lokacin wani samamen samar da tsaro da aka gudanar a Sokoto a shekarar bara, karkashin umarnin Shugaba Tinubu, wanda ta bayyana a matsayin juyin-juya hali a yaki da rashin tsaro.

Ta bayyana cewa wadannan matakai sun haifar da hallaka dumbin ‘yan bindiga, ciki ha da rikakken dan bindigar nan Halilu Sububu.

“Mun yaba wa Minista Matawalle saboda jajircewarsa da kyakkyawan shugabancinsa wajen yaki da matsalar tsaro,” inji Goronyo. “Shugaba Tinubu ya cancanci yabo saboda yarda da ya nuna wajen damka masa wannan amana.”

ƙungiyar ta bayyana cewa ci gaban tsaro ya bai wa mutane da dama a garuruwa da kauyuka damar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, ba tare da wani babban hari daga ‘yan bindiga ba, sai dai daidaiku nan da can a wasu sassa na jihohin Sokoto da Zamfara.

“Yanzu muna gudanar da ayyukanmu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, muna zuwa gona a kullum a Arewa maso Yamma ba tare da fuskantar barazanar tsaro ba,” in ji Goronyo.

ƙungiyar ta danganta wannan nasara da samame da ayyukan Rundunar Operation Fansar Yamma, wanda ta mayar da hankali wajen tarwatsa maboyar ‘yan bindiga a sassa daban-daban na yankin. An bayyana cewa ingantaccen tsaro ya saukaka zirga-zirga da kasuwanci, musamman a manyan hanyoyi kamar Zaria zuwa Sokoto da Abuja zuwa Kano.

“Wannan ci gaba ne mai burgewa. Kokarin sojoji ya saukaka sufuri da kasuwanci sosai,” Goronyo ya kara da cewa.

Sai dai duk da waɗannan nasarori, kungiyar ta nuna damuwa game da ci gaba da hare-hare a wasu kauyuka, ciki ha da Sabon Birni da Isa a jihar Sokoto, da kuma wasu sassa na jihohin Katsina, Kebbi, Kaduna, Neja da Zamfara.

“Mun san akwai kalubale a wasu wurare, amma muna da yakini cewa jami’an tsaro suna bakin kokarinsu don shawo kansu,” in ji Goronyo.

“Goyon bayan Minista Matawalle ga dakarun tsaro na da matukar muhimmanci wajen karfafa kwazonsu da ci gaba da samun irin wannan nasara.”

ƙungiyar ta kuma yaba wa Janar Musa bisa gudunmuwar da yake badawa wajen daidaita aikin rundunar sojoji don tabbatar da zaman lafiya a Arewa. Ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara daukar matakan tallafa wa sojoji da hukumomin tsaro don karfafa irin nasarorin da ake samu.

“Muna roƙon Gwamnatin Tarayya da ta kara samar da kudade don samar da karin kayan aiki domin karfafa tsaro,” inji sanarwar.

ƙungiyar ta ƙara da cewa.“Kare rayukan ‘yan ƙasa da dukiyoyinsu yana da matuƙar muhimmanci, kuma muna roƙon jami’an tsaro da su ci gaba da irin ƙoƙarin da suke yi.”

By ukarofi