Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanata Mohammed Ali Ndume Mai wakiltar Borno ta Kudu ya yi Allah-wadai da yadda naɗin muƙamai na siyasa ko na gwamnatin tarayya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi, yana nuna cewa naɗin yana fifita wani yanki ko ƙabila guda, saɓanin ƙa’idojin tsarin rabon muƙamai na tarayya.
Ndume ya ce ya yi matuƙar mamaki lokacin da ya ga jerin sunayen waɗanda aka naɗɗa a muƙaman siyasa, waɗanda suka karaɗe kafafen sada zumunta da sauran majiyoyi, yana bayyana cewa tsarin babu adalci kuma bai dace da ajandar “Sabuwar Fata” ta Shugaban ƙasa ba, wanda ya yi rantsuwar aiki da rantsuwar biyayya, inda ya sha alwashin haɗa kowa da kowa a tafiyar da gwamnati.
Ndume ya bayyana hakan ne a wani shiri na Arise News (Prime Time) ranar Litinin.
Ya jaddada cewa a matsayinsa na dan majalisa kuma bisa ga abin da ya lura da shi, nadin muƙaman da Shugaba Tinubu ya yi zuwa yanzu sun saɓa da tsarin rabon muƙamai na tarayya, kuma ya kamata a gyara hakan.
Sanatan, wanda ɗan Jam’iyyar APC mai mulki ne, ya kasance mai magana kai tsaye kuma mai sukar wasu manufofi da shirye-shiryen gwamnati da ake zargin ba su amfani talakawan Nijeriya da masu kaɗa ƙuri’a ba.
