Sulaiman Bichi da Iliyasu Kwankwaso sun kama aiki a Hukumar Kogunan Haɗejia Da Jama’are

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Al’umma daga ƙananan hukumomin Madobi da Bichi sun raka sabbon manajan daraktan Hukumar Kogunan Haɗejia da Jama’are, tsohon sakataren gwamnanatin Jihar Kano Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi da Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso sabon babban daraktan kuɗi da mulki a hukumar da wasu ƙarin muƙamai uku bayan naɗin da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya  ya yi wa mutum biyar sabbin muƙamai a hukumar da suka kama aiki.

A ranar Talata ne sabbin shugabannin suka kama aiki bayan da masoya da magoya bayansu suka yi musu rakiya ta musamman domin shaida yadda za su kama aikin.

A jawabin sabon shugaban hukumar, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi, ya yi alƙawari ga al’ummar  jihohin Kano/Jigawa da Bauchi na inganta harkokin noma da kuma samar da  aikin yi ga ɗimbin matasa kasancewar ma’aikatar babba ce, za su yi amfani da ita wajen tallafawa ‘yan jam’iyyar APC, za su zo da tsare-tsaren da tallafi da zai kai ga kowa.

Sabon Manajan Daraktan na hukumar kogunan Hadejia da Jama’are, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi ya ce akwai tsare-tsare na noman zamanin da zai kyautata shi da za a riƙa yin noma a gida  kuma a riƙa yin fiye da sau biyu a shekara, da hakan zai amfani masu ƙaramin ƙarfi kuma ya haɓaka tattalin arziki.

Ya nemi haɗin kai da goyon bayan ma’aikatan hukumar da sauran al’umma ta yadda za a haɗu a ciyar da ma’aikatar gaba yadda za ta amfani al’umma. Sannan ya gode wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa ba su wannan muƙamai.

A nasa jawabin, Babban Daraktan Kuɗi da Mulki na Hukumar Raya Kogunan Hadeja-Jama’are, Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce, zai yi iyaka ƙoƙari, don inganta rayuwar al’ummar jihohin Kano Jigawa da Bauchi.

Ya kuma gode wa masoya da magoya baya da suka rako su ma’aikatar, domin kama aiki, inda ya bayar da tabbacin za su ɓullo da tsare-tsare na kyautata wa magoya baya sosai, sannan ya yi kira da a taya su da addu’a kan Allah ya ba su ikon sauke nauyin da Shugaban ƙasa ya ɗora musu.

By ukarofi