Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin jihohin Nijeriya sun gargaɗi ciyamomi kan buɗe asusu a Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin biyan kuɗaɗen kason su kai tsaye daga asusun tarayya.
Wannan koma baya na zuwa ne kusan watanni tara bayan da Kotun ƙoli ta bada cikakken ikon cin gashin kai ga ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasar nan, tare da share fagen biyan kuɗaɗen kason da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa kai tsaye.
A wani angare na ƙudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da hukuncin kotun koli, an kafa kwamitin da zai tabbatar da aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomin.
A bisa shawarar da ya bayar, kwamitin ya umurci babban bankin Nijeriya da ya buɗe asusu na ƙananan hukumomi 774 domin biyan su kason su kai tsaye.
A kwanakin baya ne Babban Akanta Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein da Babban Lauyan Majalisar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, da sauran jami’ai suka fara tattaunawa kan yadda ƙananan hukumomin za su buɗe asusun ajiya da CBN don rabon kuɗaɗen kai tsaye amma rahotanni sun ce suna fuskantar ƙalubale wajen tantance ƙananan hukumomin da aka zaa ta hanyar dimokraɗiyya.
Wani taron kwamitin fasaha na kwamitin rabon kuɗaɗen asusun tarayya ya nuna cewa ƙananan hukumomin jihar Delta ne kawai suka miƙa bayanan asusun su.
Sai dai wasu shugabannin ƙananan hukumomin da suka zanta da jaridar Punch, sun bayyana cewa wasu gwamnonin sun koma tursasa su da janye, inda suka matsa musu lamba da su guji buɗe asusun da aka kee domin biyan su kai tsaye.
Wani shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa wani gwamna a yankin Kudu-maso-Gabas ya ƙi karɓar kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da ake kashewa duk wata, wanda hakan na cikin yarjejeniyar da aka ƙulla da nufin sauƙaƙa buɗe asusun ajiyar kuɗi kai tsaye.
“Gwamnan mu ya yi mana barazana (dukkan shugabannin ƙananan hukumomin jihar) da kada mu buɗe asusu a bankin CBN domin biyan mu kason kai tsaye.
“Mun ma yi ƙoƙarin roƙonsa, muna neman aulla yarjejeniya, ta yadda idan har ya ba mu damar buɗe asusun ajiya da CBN, kuma an biya kason mu kai tsaye, za mu riƙa ba shi kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen duk wata, amma bai yarda ba, don haka a nan ne muke a halin yanzu,” inji Shugaban ƙaramar hukuma.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa wasu da dama daga cikin gwamnonin na adawa da buɗe asusun bankin na CBN, saboda fargabar ya raba musu kuɗaɗen ƙananan hukumomi da suka daɗe suna yi.
