Sace ɗalibi: Gwamnatin Kebbi ta yi alƙawarin inganta tsaro a makarantu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya yi kakkausar suka kan sace Augustine Madubiya, ɗalibi a matakin 400 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi (FUBK), wanda wasu ’yan bindiga da ba a tantance ba suka yi garkuwa da shi da sanyin safiyar Talata.

Abin takaici, maharan sun harbe wani mazaunin unguwar mai suna Malam Siddi Hussaini a lokacin da suke ƙoƙarin kuɓutar da ɗalibin.

Sanarwar da Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa Abdulrahman Zagga ya fitar ta ce gwamnatin jihar Kebbi ta ɗauki matakai cikin gaggawa don ganin an sako wanda aka yi garkuwa da shi lafiya.

Gwamna Idris ya umurci ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su haɗa kai da hukumomin jami’ar domin ganin an sako ɗalibin da aka sace.

Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Unguwar Jeji da ke ƙaramar hukumar Kalgo, musamman iyalan marigayin, da kuma al’ummar FUBK.

Ya kuma bai wa iyaye da ɗaliban tabbacin cewa, gwamnati tana jajircewa wajen tabbatar da tsaron su.

Daraktan tsaron ya kuma bayyana cewa, lamarin ya faru ne a Istijaba ɓilla, wani gidan kwanan ɗalibai da ke unguwar Jeji, amma ba a cikin harabar jami’ar ba.

By ukarofi