Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Lafiya na Nijeriya, Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci 16,000 sun fice daga Nijeriya cikin shekara biyar ko shida.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙara wa juna sani na ƙungiyar likitoci ta ‘Association of Medical Councils of Africa’ (AMCOA) ranar Talata, yana mai cewa hakan ya jawo wa ƙasar asarar biliyoyin naira.
Ya ce ƙiyasin kuɗin da ake kashewa wajen bai wa likita ɗaya horo a Nijeriya ya zarta dala 21,000, inda ya nuna damuwa game da yadda Nijeriya ke asarar irin waɗannan kuɗaɗe.
“Wannan lamari ba wai magana ce kawai ta mutanen da ke ficewa ba, hakan na nufin asara,” inji ministan.
“Yana shafar ɓangaren kula da lafiyarmu sosai, inda yankunan ƙauyukanmu suka fi shiga haɗari.”
Ya ƙara da cewa, yanzu yawan mutanen da likita ɗaya ke gani a Nijeriya ya ƙaru zuwa miliyan 3.9, wanda ya zarta adadin da hukumar lafiya ta duniya ta ƙiyasta sosai.
