
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinsa na fitar da ɗalibai da suka yi karatu a ƙasashen waje daga ƙunci, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya warware matsalolin da suka sanya aka riƙe musu takardun shaidar kammalawa.
Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar.
Ya ce, tun a watan Disambar 2024 ne gwamnan ya je Cyprus da nufin samar da mafita ga matsalar, wadda gwamantin baya ta gaza saukewa.
A yayin ganawa da wakilan Jami’ar ‘Near East University’, Gwamna Abba ya mayar da hankali ne akan sake wa ɗaliban da suka kammala karatu daga shekarar 2015 zuwa 2019 musamman ƴan ɓangaren likitanci takardunsu.
A nan gwamnan ya kashe kimanin Naira biliyan 2.5 ga ɗalibai 84 ƴan sahun shekarun 2015 zuwa 2019. Lamarin da ya sake jefa ɗaliban cikin farin ciki tare da sanya tsammani game da gobe mai kyau da suke fatan samu.
Ibrahim Adam ya kuma ce, za a bada takardun ga Hukumar Bada Tallafin karatu ta Jihar Kano don isar da su ga ɗaliban da hakan ya shafa.
Ana ganin matakin ya nuna yadda gwamnan ke ƙoƙarin fifita ɓangaren harkar ilimi a jihar ganin yadda ake sa ran matasan za su taimaka wajen ciyar da jihar gaba.
