Samun N1500 kullum kuɗi ne mai yawa, inji mashawarcin Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai baiwa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin tattalin arziki, Dr Tope Fasua, ya kare darajar Naira duk da rauninta a kan dala, yana mai cewa dala 1, kwatankwacin sama da N1,500, na iya sayen abinci mai yawa a Nijeriya.

Dokta Tope Fasua, mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin tattalin arziki, ya bayyana hakan yayin wani na Mic On Podcast.

“Dala 1 shi ne N1,500. Samun dala 1 a kowace rana, wannan kuɗi ne mai yawa ga ‘yan Nijeriya da yawa,” Fasua ya bayyana cikin kwarin gwiwa yayin da yake ƙoƙarin rage damuwar da ke ƙara ta’azzara taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu.

Ya ci gaba da cewa: “Hakan ya kai mu wajen sayen wutar lantarki, kuma abin da ya kamata mu duba ke nan, dala 10 ba za ta saya muku abincin rana a ko ina a Amurka ba, kana buƙatar aƙalla dala 20. Wato kusan N30,000. Amma zan iya gaya maka abin da za ka iya yi da dala 5, wato N7,500 a Nijeriya.”

“Idan ba za ku ci abinci a wuraren cin abinci masu tsada ba, akwai abubuwa da yawa da N7,000 za ta iya yi,” inji shi.

“A Gwarinpa akwai masu sayar da gasashen plantain da kifi a bakin hanya, za ku ci abincin Naira 1,500, ku ƙoshi, babu takura kai.”

“Babu wani wuri a duniya da mutane ba sa shan wahala. Babu tattalin arziki da ba za ku sami mutanen da ke shan wahala ba,” inji shi.

Ya yi watsi da ma’aunin talauci na duniya da aka yi amfani da shi wajen tantance adadin ‘yan Nijeriya da ke fama da matsanancin talauci, yana mai cewa ba sa amfani yadda ya dace.

By ukarofi