Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban ƙaramar hukuma a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

‘Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara Alh Saminu Sulaiman Morai.

Wani mazaunin yankin mai suna Abdulrahman Sulaiman Morai a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja ya bayyana wa wakilin mu.

A cewarsa, Marigayi Saminu Morai, an kashe shi ne a lokacin wani hari da wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka kai wa al’ummar yankin a daren jiya.

“‘Yan ta’addan sun yiwa yankin ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:00 na daren jiya ɗauke da manyan makamai tare da yin yunƙurin yin garkuwa da marigayin shikuma yaƙi amincewa da buƙatar su wanda hakan ya sa suka harbe shi har lahira”. Yace

Ya kuma bayyana cewa an sace matarsa da ‘ya’yansa da wasu mutanen wanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba a yayin harin.

Saminu Morai ya kasance babban sakataren dindindin mai ritaya, bayan haka ya zama shugaban Ƙaramar hukumar Talatar Mafara na riƙon ƙwarya.

“Kamar yadda nake magana da kai a yanzu, har yanzu ba mu da tabbacin adadin mutanen da waɗannan ‘yan ta’addan suka sace a lokacin harin’.

A cewarsa, a yau ne za a yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Yazid Abubakar daga wakilin mu akan lamarin hakan yaci tura har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

By ukarofi