Ziyarar Faransa: Kace-nace ya ɓarke tsakanin Tinubu da Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tun bayan da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi ziyarar aiki ƙasar Faransa, ake samun kace-nace tsakanin gwamnatinsa da ’yan adawa da ma masu lura da al’amuran yau da kullum a ƙasar da wajenta, inda yayin da wasu ke kare balaguron nasa, wasu kuwa suka suke yi.

A baya-bayan nan tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ne ya buɗe ƙofar kace-nace tsakaninsa da Gwamnatin Tinubu bisa sukar da ya yi na cewa, ya yi watsi da ’yan Nijeriya a daidai lokacin da ake ta faman kashe su a sassa daban-daban na ƙasar.

Sai dai kuma nan take Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da martani, inda ta ce, Shugaba Tinubu yana da ƙwarewa da basirar da zai iya gudanar da mulkin ƙasar a ko’ina ya ke a faɗin duniya.

Tinubu na da ƙwarewa ta mulkar Nijeriya daga wajenta – Fadar Shugaban ƙasa:

Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da martani kan sukar da ake yi wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ta ce duk da ba ya ƙasar, yana sa ido sosai kan abubuwan da ke gudana.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Yayin da ake ta kashe-kashe da garkuwa da mutane, jiga-jigan ‘yan adawa sun buƙaci Tinubu ya dawo gida da gaggawa.

Duka Atiku Abubakar da Peter Obi, waɗanda su ne manyan abokan hamayyar Tinubu a zaɓen 2023, sun ce ci gaba cewa zaman shugaban ƙasar a ƙasashen waje bai dace ba.

Amma Onanuga ya kare shugaban nasa, yana mai cewa shugaban “ya lura da komai cikin harkokin mulkin Nijeriya duk yana Turai.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da sa ido kan arkokin mulkin Nijeriya duk da cewa yana Turai.

“Shugaban ya bar Paris zuwa Landan a ƙarshen mako kuma ya ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an gwamnati, yana sa ido kan muhimman al’amuran ƙasa, gami da umarni ga shugabannin tsaro don magance barazanar da ke kunno kai a wasu sassan ƙasar.

“Komawarsa Abuja da kuma ci gaba da aiki a Aso ɓilla zai biyo bayan kammala hutun Ista, yana jajircewa kan ayyukansa duk da ba ya nan, kuma gwamnatinsa na ci gaba da aiki yadda ya kamata a ƙaraashin jagorancinsa.

“Mun yaba da damuwar jama’a kuma muna tabbatar wa dukkan ‘yan Nijeriya cewa mulki yana tafiya ba tare da matsala ba.”

Tinubu ya yi shakulaton ɓangaro da nauyin da aka ɗora masa – Atiku:

Jagoran ‘yan adawar siyasa a Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana ziyarar aiki da Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ke yi a ƙasar Faransa a matsayin ‘mummunan watsi da aikinsa’ na Shugaban ƙasa yayin da ƙasar ke fama da manyan ƙalubale.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Paul Ibe, wanda aka wallafa a shafinsa na ɗ.

Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan adawa a Nijeriyar ke ci gaba da sukar matakin da Bola Tinubu ya ɗauka na kasancewa a ƙasar Faransa duk kuwa da abubuwa na rashin tsaro da ke haifar da kashe-kashe a Nijeriya.

A farkon watan Afrilu ne shugaban na Nijeriya ya bar ƙasar zuwa Faransa domin gudanar da wata ziyarar aiki, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.

Sai dai tun bayan tafiyarsa an kai munanan hare-hare a jihar Filato, waɗanda suka yi sanadiyyar kashe fiye da mutum 100.

A cikin sanarwar da ya fitar, Atiku ya ce “wane dalili (Tinubu) ke da shi na ci gaba da karaɗe ƙasashen Turai bayan ana zubar da jini a Nijeriya?

“Yayin da Tinubu ke cin gara a ƙasaitattun wurare, ƙasar da yake jagoranta ta faɗa tsundum cikin yamutsi,” inji Atiku.

Ya ƙara da cewa “idan har Tinubu na da tausayi, to ya kamata ya katse tafiyarsa ya koma gida ba tare da ɓata lokaci ba.”

Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan sukar da ɗan takarar shugaban Nijeriya a jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi wa Tinubu kan tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake samun hare-haren da ke haifar da asarar rayuka a ƙasar.

A sanarwar da fadar shugaban ƙasar ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga a ranar biyu ga watan Afrilu ya ce a lokkacin ziyarar ta Tinubu zuwa Faransa, “zai yi nazari kan ayyukan gwamnatinsa da kuma nasarorin da ya cimma.

Haka nan kuma zai yi amfani da lokacin wajen nazari kan sauye-sauyen da ya kawo sannan ya fara shirye-shirye kan bikin cikarsa shekaru biyu kan mulki.”

By ukarofi