Tinubu ya kafa kwamitin tsara yadda za a gudanar da ƙidayar ‘yan Nijeriya

Spread the love

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rantsar da kwamatin da zai tsara yadda za a gudanar da ƙidayar ‘yan ƙasa a ranar Laraba.

Shugaban wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya wakilta ya bai wa ‘yan kwamatin wa’adin mako uku da su gabatar da rahotonsu.

Karo na ƙarshe da Nijeriya ta ƙidaya ‘yan ƙasa shi ne a 2006, inda ƙididdigar ta nuna 140,431,790, inda aka samu maza 71,345,488 da mata 69,086,302.

Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu ya alaƙanta ƙidayar da cigaban ƙasa.

“Ku yi aiki da dukkan hukumomin da suka dace, ciki har da ma’aikatar kasafi. Dole ne wannan ma’aikatar ta jagoranci aikin saboda ba za ka iya yin kasafi ba idan ka san yawanmu ba,” inji shi.

By ukarofi