Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin wucin gadi da ke kula da lamarin Jihar Ribas ya gayyaci Kantoman riko na jihar, ɓice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya.), da ya bayyana a gabansu ranar Alhamis domin gudanar da zaman tattaunawa.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Akin Rotimi (Jnr), ya fitar a ranar Laraba.
Manhaja ta rawaito cewa, kwamitin da ke da mambobi 21, ƙarƙashin jagorancin shugaban masu rinjaye na Majalisar, Farfesa Julius Ihonɓbere, an kaddamar da shi ne a ranar Talata daga Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen.
Majalisar Wakilai ce ta kafa kwamitin biyo bayan kudurin da Majalisar Tarayya ta amince da shi, wanda ke goyon bayan ayyana dokar ta-baci da Shugaban ƙasa ya yi a Jihar Ribas.
A cewar Rotimi cikin sanarwar, an fitar da gayyatar ne a zaman farko da kwamitin ya gudanar a ranar Laraba, bayan kaddamarwar da Shugaban Majalisar ya yi a ranar Talata, 15 ga Afrilu, 2025.
Ya bayyana cewa zaman ya ba da damar tattauna rahotannin farko da abubuwan da ke faruwa tun bayan da kantoman ya hau mulki a Jihar Ribas.
