
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon ministan shari’a kuma Antoni-Janar na ƙasa, Dakta Abubakar Malami (SAN), ya yi watsi da ikirarin da ƴan ƙungiyar Sanata Umaru Tanko Al-Makura suka yi na cewa mambobin tsohuwar jam’iyyar CPC dake APC sun fasa ficewa daga jam’iyyar tare da amince wa mara wa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Malami ya faɗi hakan ne ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Muhammad Bello Doka, inda ya ce tawagar CPC wanda ɓangare ne na tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ita ke da alhakin bayyana ra’ayinta ba ɓangaren Al-Makura ba.
Ya ce, kalaman nasu bai shafin ɓangaren ba da ake kira da ‘CPC blog’, ya na mai cewa sun yi hakan ne don cimma wata manufar siyasa daga ɓangaren APC.
Game da jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar SDP kuwa, Malami ya ce batun ba gaskiya bane, wanda an ƙirƙire ta ne don cimma wata manufa.
Ya ƙara da cewa, a matsayin Malami na ɗan siyasa, zai bayyana ficewar sa ne yayin da hali ya bada dama tare da sanar da sauya sheƙarsa a lokacin da ya dace.
