Muhimmancin Abuja ya wuce a bar ta hannun ƴan adawa, inji Ganduje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce muhimmanci Birnin Tarayya Abuja ya wuce a bar ta a hannun jam’iyyun ɓangaren adawa.

Ganduje ya faɗi haka ne ranar Alhamis a Abuja a yayin karɓar wasu sababbin mambobin APC da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun PDP, LP da wasu.

Shugaban ƙaramar hukumar birni (AMAC), Chris Maikalangu ya jagoranci tawagar a tsohon filin fareti dake Abuja.

Ya ce, hakan ya nuna yadda masu zaɓe suka gamsu da APC a birnin kuma yana fatan za su yi ruwan kuri’u ga jam’iyyar don sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Ya bayyana cewa, bai kamata a bar wa ƴan adawa Abuja ba ganin cewa ita ce cibiyar haɗuwar al’ummar Nijeriya.

Ya kuma ce, daga cikin nasarorin da al’ummar birnin suka samu shine bai wa ƴaƴanta muƙamai a gwamanti da Shugaba Tinubu ya yi, wanda hakan ya ja ra’ayoyi ƴan siyasa shiga APC.

Ya ƙara da cewa, APC ta na cigaba da samun karɓuwa a Abuja da wasu sassan Nijeriya.

By Babaji