Hanyoyin magance faɗan daba da matsalar ‘yan Sara-Suka a Jos

Spread the love

Daga HASSAN IMRAN 

Ranar ƙarshe ta watan Maris da ya gabata wacce ta yi daidai da ranar da al’ummar Musulmi suka gudanar da murnar bikin ƙaramar Sallah, bayan kammala azumin watan Ramadan. Wani abin takaici da ban haushi ya faru a garin Jos, musamman a unguwannin cikin gari inda Hausawa suka fi rinjaye.

Wasu matasa ‘yan daba waɗanda aka fi sanin su da ’yan Sara-Suka suka ɗauki makamai irinsu wuƙaƙe suke yaƙar junansu. ’Yan dabar unguwar A suna yaƙar ’yan dabar unguwar B. Abin ya yi muni ta yadda har ta kai ga wani a cikinsu bai isa ya shiga wata unguwar da ba tasa ba. 

An rawaito cewa, waɗannan yara ɓatagari sun kashe aƙalla mutane uku, kuma suka raunata juna da dama. A lokacin da malamai suke ƙoƙarin jan hankalin al’umma da su wa’azantu da darussan da watan Ramadan ya karantar da mu, kamar su haƙuri, tsoron Allah, kiyaye munanan ayyuka da kuma taimaka wa juna akan ayyukan alkhairi, su waɗannan matasa basu samu tasirin waɗannan darussan ba. 

Wannan masifar ta faɗan Daba da ‘yan Sara-Suka suke yi, ya matuƙar tayar wa jama’a a Jos hankali, inda kowa ke Allah wadai da irin wannan mummunar ɗabi’a. Bugu da ƙari, wannan ta’addancin ‘yan Sara-Suka ya fi muni a duk lokacin da ake bukukuwan sallah. 

Garin Jos na ɗaya daga cikin garuruwan da yake fuskantar matsalolin rikice-rikice masu nasaba da siyasa da kuma addini, amma cikin ikon Allah ana samun sauƙin abubuwa. Bai kamata a ce lokacin da mutane ke jin daɗin zaman lafiya da lumana ba a samu matasa marasa tunani da za su riƙa tayar da zaune tsaye, ko aikata wasu ayyukan ta’asa ga juna ba.

Masana sun yi bayani cewa matasa su ne jigon (pillar) gina kowacce al’umma. Babu al’ummar da za ta samu cigaba ko nasara face sai ta kasance tana kula da tarbiyyar matasan ta. Haka zalika, babu al’ummar da za ta kasance a ƙasƙance ko cikin rauni, face matasan ta sun kasance ƙasƙantattu ɓatatatu.

Wannan na cikin dalilan da suka sa addinin Musulunci ya bayar da gagarumin muhimmanci akan tarbiyyar matasa. Mafi yawan sahabban Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama, da suka wa Musulunci hidima har ya iso gare mu matasa ne. Manzon Allah ya bayar da kulawa sosai wajen tarbiyyantar da matasa a lokacin sa. Ya taɓa naɗa wani matashi mai suna Usamatu bin Zayd -wanda a lokacin shekarar sa goma sha takwas- ya jagoranci rundunar Musulunci wacce za ta gwabza yaƙi da mutanen da suka fi kowa ƙarfin mulki da kuma sojoji a lokacin. Ire-iren waɗannan matasa su ne suka ciyar da Musulunci gaba ta hanyar yaɗa karantarwar sa a saƙo da saƙo, lungu da lungu har ya zama gama gari.

Shin za mu iya danganta matasa na yau cewa jikokin waɗancan matasa na lokacin Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ne?

Daga cikin dalilai da ke janyo wannan faɗan daba na ‘yan Sara-Suka akwai rashin samun ingantacciyar tarbiyya da kuma rashin kulawar iyaye akan tarbiyyar ‘ya’yansu. Har wa yau, akwai matsalar shan miyagun ƙwayoyi da kuma wasu rashin kunya da koyi da matasa ke yi da jaruman finafinai da kuma shafukan sada zumunta. 

Haƙƙin ne akan iyaye su kula da tarbiyyar ‘yan’yansu domin amana ce da Allah ya rataya a wuyar iyaye. Goya wa ‘ya’ya baya akan laifin da, suka aikata, na ƙara ingiza su su zama maɓarnata kangararru. Har wa yau, wajibi ne iyaye su bada kulawa ta gaske ga abokai ko ƙawayen da ‘yan’yansu ke mu’amala da su. Bai wa matasa ingantaccen ilimi da kuma ilimin sana’o’in hannu na da matuƙar muhimmanci da yakamata Gwamnati ta maida hankali akan haka sosai. Hukumar masu yaƙi da miyagun ƙwayoyi yana da kyau su ƙara ƙaimi wajen ilimintar da matasa akan illolin ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi. Sa’a nan su sani cewa duk ɗan shaye-shaye hatsari ne ga al’umma. Masu shan kayan maye da masu zaman kashe wando su ne mafi yawan matasan da, suka fi shiga harkar Sara-Suka wanda ya kamata hukumomi su ɗauki ƙwararan matakai akan su, ta hanyar hukunta su domin su zama izina ga sauran.

Allah Ya taƙaita mana masifu ya kuma shige mana gaba a harkokin mu. Allah Ya shirya mana matasan mu maza da mata, Ya zaunar da ƙasar mu lafiya. Amin. 
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected]

By ukarofi