Ya kamata gwamnonin Arewa su ɗauki matakai na bunƙasa yankin

Spread the love

Daga JABIRU HASSAN

Duk da irin ƙoƙarin da gwamnonin arewacin ƙasar nan ke yi, akwai buƙatar su ƙara himma wajen ɓullo da shirye-shirye waɗanda za su bunƙasa yankin ta fannoni daban-daban.

Yanzu lokaci ya yi da gwamnoninmu za su zamo masu ƙoƙarin kafa managarcin ginshiƙin farfaɗo da yankunansu bisa la’akari da buƙatun kowane ɓangare kamar yadda muke gani a ƙasashen da suka ci gaba.

A yankinmu na arewacin ƙasar nan, akwai mabambantan buƙatu da ke kowane sashe da kuma kowane ɓangare waɗanda idan aka sami nasarar aiwatar da su za a kasance cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Akwai abubuwa da suka kamata gwamnoninmu da masu riƙe da madafun ikon yankin Arewa su samar a yankin, domin samun nasarar kyautata rayuwa da tattalin arziki al’umma kuma cikin sauƙi da nagarta.

Kowa dai ya san cewa yankin arewacin ƙasar nan yana da dukkanin abubuwan da za a yi amfani da su wajen inganta rayuwar al’umma kamar madatsun ruwa da ma’asinai da ƙasar noma da kiwo da kuma abubuwan sarrafawa da mafiya yawan kamfanonin da ake da su suke buƙata.

Idan muka ɗauki batun madatsun ruwa, za mu ga cewa kafin a bar ƙananan dam da ake da su a gurare daban-daban ana gudanar da noman rani da kiwon dabbobi a sassan da suke da ire-iren waɗannan ƙananan madatsun ruwa a yankunansu, kuma a wancan lokacin, an sami tattalin arziki da kwanciyar hankali fiye da yadda abin ya ke a yau.

Haka kuma a jihohin da suke da ma’adinai ana gudanar da hakan su da cinikayyarsu wanda hakan ya haifar da alheri sosai kafin daga baya abubuwa suka lalace baƙin haure suka shigo kuma suka lalata wannan harka wadda a yau ɗin nan lamarin harkar ma’adinai ta zamo barazana ga tsaron ƙasa, saboda son zuciya.

Sannan idan muka waiwayi harkokin cinikayyar fatu da kira ga ita ma shugabannin namu na yankin Arewa sun bari waɗanda ba ’yan ƙasa ba sun dabaibaye harkar tare da mayar da ’yan ƙasa ba yi marasa ikon komai a wannan fanni.

Dangane da harkar sufuri da harkokin kayan amfanin gona nan ma dai an bari wasu sun karɓe harkokin, inda a mafiya yawan manyan kasuwannin hada-hadar kayayyakin abinci suke dama da matsalolin baba-kere na baƙi wanda hakan ya taimaka wajen mayar da ’yan ƙasa aniyar ware duk da cewa suke da abin.

Lokaci ba zai bari a fayyace irin illolin da yankin Arewa ke fuskanta ba, amma dai ba a makara ba kuma idan an so za a iya gyara abubuwa, domin ganin yankin ya sake farfaɗowa fiye da wancan zamani da ake ganin daraja da martabar yankin.

Kafin na kammala wannan ra’ayi nawa, zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnoninmu na Arewa da su bari a aiwatar da tsaron nan na bai wa majalisun ƙananan hukumomi kuɗaɗen su da ake ba su daga asusun tarayya, domin ɗaukar nauyin al’umomin yankunansu.

Bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye zai kawo sauyi ta fuskar tsaro da samar da ayyukan yi musamman ga matasa maza da mata, sannan zai sanya a samar da ayyukan yi, domin sauke hankalin matasan daga tunanin faɗa wa cikin wasu hanyoyi na jaddada rashin zaman lafiya.Daga ƙarshe, Ina ƙara jaddada cewa, gwamnoninmu na Arewa za su iya haɗa hannu wajen kawar da dukkanin wasu abubuwa da ke haifar da rashin tsaro a yankunansu, sannan sun san cewa lokaci ya yi da za su fara aiki da murya ɗaya, domin magance mafiya yawan matsalolin yankin.

Jabiru Hassan shine ko’odinetan shirin Media Action kuma za a iya samun sa ta: [email protected]

By ukarofi