
Daga BELLO A. BABAJI
A yau Litinin ne aka samu cincirindon al’umma a Jos, babban birnin Filato sun fito zanga-zanga don nuna damuwarsu game da kashe-kashe da ke faruwa a wasu sassan jihar, wanda ake zargin ƴan bindigar Fulani da aikatawa.
Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen jihar, Reberen Polycarp Lubo da wasu jagororin addinin ne suka jagoranci zanga-zangar.
A gano masu gangamin ɗauke da alluna da wasu ababe da ke nuna kaɗuwarsu da aukuwar hare-haren, inda suka cika manyan titina tare da haddasa cinkoso.
Suna kira ne ga gwamnatin jihar da ta gaggauta tsoma baki a lamarin tare da kawo ƙarshen munanan ayyukan a jihar.
