Daga MUKHTAR A. HALLIRU Sakkwato
Shugabar rukunin makarantun Ummuhatul Ummah Al-Islamiyya Gidan Kuka Runjin Sambo, Malama Khadija Muhammad Bajini Galadanci ta yi kira ga al’ummar Musulmi su riƙa yi wa shugabanni addu’o’in alheri a maimakon yawan aibata su da yi musu mummunan fata.
Malama Khadija wacce ke cikin ƙalilan ɗin malamai mata da ke cikin garin Sakkwato, ta yi wannan tunatarwa ne a wata zantawa da ta yi da manema labarai. Ta kuma bayyana damuwar ta game da yadda al’umma suka shagaltu da zagin shugabannin al’umma, ýan siyasa da malamai wanda bai dace ba, kuma ba zai kai al’umma ga mafita ba.
Malamar har wayau, ta bayyana yadda abokan zaman mu na kudancin ƙasar nan da wuya ka ga sun fito zaurukan sada zumunta suna cin mutunci da zagin shugabanninsu. Don haka ta bada shawara kan cewa me zai hana idan mun ga shugaba yana abin da ba daidai ba a samu na kusa da shi, a sanar da su abubuwan da suke yi da bai dace ba. Sannan a riƙa yi musu addu’ar shiriya da fatan alheri.
A ɓangaren shugabanni da malamai, Malama Khadija ta shawarce su da su tsare girma da kimar su, kuma su guji duk wani abu da zai iya zubar musu mutuncinsu a idon al’umma.
Malama Khadija Bajini Galadanci ta yi kira ga al’ummar Musulmi su yi ƙoƙarin ganin sun cigaba da aiwatar da kyawawan ayyukan da suka koya cikin watan Ramadan, kuma su himmatu don ganin su samu yin azumin Sitta-Shawwal, domin samun garaɓasar da ke a ciki. Malamar ta yabawa Gwamnatin Jihar Sakkwato akan yadda ta ɗauki nauyin ciyarwa cikin watan azumi, da yabawa ga Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi akan hidimar da ake yi wa ayyukan addinin Musulunci a koda yaushe.
Malama Khadija ta kwashe shekaru tana gabatar da Tafsirin Alƙur’ani cikin Watan Ramadan, da kuma karantar da mata a makarantun ta sama da shida da ke cikin ƙwaryar birnin Sakkwato.
