Hukumar kashe gobara a Kano ta magantu bisa gobara a Rijiyar Zaki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta yi tsokaci kan kiraye-kiyaren da ta samu game da ɓarkewar gobara a Kwanar Ƴan Kifi dake Unguwar Rijiyar Zaki a ranar Lahadi.

A sanarwar Kakakinta, Saminu Yusuf Abdullahi, hukumar ta ce wani gida da ake harkokin kasuwanci aciki mai faɗin ƙafa 100 da 50 ne ya kama da wuta.

Lamarin da ya yi sanadin ƙonewar shaguna uku, motoci uku da wasu ajijuwa bakwai na makarantar ‘Young Marshall Science Academy’ da wani sashinta.

Wani shaida ya bayyana cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mutane daga wata mota ƙirar J5 mara rajista suka fitar da tukwanan gas tare da jibge su a wani shago, inda daga nan suka fara ci da wuta tare da ƙone shaguna da motoci.

Kakakin ya ce, jami’an hukumar daga hedikwatarta da wasu a Rijiyar Zaki da Bompai ne suka kai ɗauki tare da samun nasarar kashe gobarar.

Ya kuma ce, ba a samu rahoton mutuwa ko jin rauni ba daga cikin jama’ar wajen, ya na mai cewa ana gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar al’amarin.

By Babaji