Mun yi rashin ƙaƙƙarfar muryar yaƙi da zalunci, inji Tinubu bisa rasuwar Paparoma

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar Paparoma Francis, yana mai cewa duniya ta rasa ɗaya daga cikin mafiya tasiri wajen yaƙi da rashin adalci. A wata sanarwa mai cike da tausayawa, Tinubu ya bayyana Paparoma a matsayin bawan Allah mai tawali’u da kuma mai tsayawa tsayin daka wajen kare talakawa da waɗanda aka manta da su.

Shugaba Tinubu ya ce mutuwar Paparoma bayan bikin Easter alama ce ta dawowarsa ga Mahaliccinsa cikin lokaci mai ma’ana ga mabiya addinin Kirista. Ya yi kira ga ’yan Najeriya da al’ummar duniya su girmama Paparoma ta hanyar ayyuka na alheri, adalci da haɗin kai maimakon kalmomi kawai.

Bugu da ƙari, Shugaban ƙasa ya yabawa jajircewar Paparoma wajen kira ga shugabanni su yi adalci, da goyon baya ga marasa galihu da masu gudun hijira. Ya ce Paparoma Francis ya kasance murya mai ƙarfi wacce ke ƙarfafa zaman lafiya, kare muhalli, da kuma jaddada ’yancin ɗan adam a duniya. Tinubu ya yi addu’ar Allah ya karɓi Paparoma cikin rahamarsa.

By ukarofi