Umartar al’umma su kare kawunansu ba daidai ba ne – Martanin Gwamnan Jigawa ga TY Ɗanjuma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi ya yi tsokaci game da kalaman tsohon babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Theophilus Ɗanjuma na kira ga ƴan ƙasa da su ɗauki matakan kare kawunansu ganin yadda rashin tsaro ya tsananta a ƙasar.

Gwamnan, a wata hira da gidan talabijin na ‘channels’, ya ce kalaman za su iya kai al’umma ga taka doka a yayin da suka ɗauke ta a hannayensu.

Ya ce, a matsayin TY Ɗanjuma na babban masanin harkar tsaro da ya kamata a girmama, ba daidai bane ya furta irin kalaman, waɗanda ka iya haddasa bijirewa dokokin da aka amince da su a ƙasa.

Namadi ya ce, lallai akwai buƙatar a yi nazarin kalaman nasa cikin kulawa musamman la’akari da ƙoƙarin gwamanti na ganin ta inganta harkokin tsaro a ilahirin sassan Nijeriya.

Ya kuma bada misali da jiharsa ta Jigawa, inda al’umma a matakai daban-daban suka bada haɗin-kai tare da wasu shirye-shirye da gwamantinsa ta samar, waɗanda suka taimaka wajen rage aukuwar rikici a jihar.

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ta goyi bayan kafa ƴan sandan jihohi, waɗanda a cewarsa, za su taimaka wajen daƙile matsalolin tsaro da ke addabar al’umma a sassa daban-daban na ƙasa, don haka lokacin.

“Ba mu kai matakin da ake buƙatar al’umma su kare kawunansu ba”, inji gwamnan.

By Babaji