An samu mataimakiya ga Gwamnan Delta a mace, yayin da ake tuhumar mijinta da hannu a mutuwarta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan Jihar Delta ta fara gudanar da bincike game da musabbabin mutuwar Love Shimite Bello, wadda ita ce mai bai wa Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar shawara kan harkokin kasuwanci.

A safiyar ranar Litinin ne Shimite ta rasu.

A karon fari rahotonni sun bayyana cewa ta rasu ne bayan fama da wani gajeren rashin lafiya, yayin da daga bisani wani shaida ya ce an gano gawarta ne a wani mummunan yanayi.

Kakakin ƴan sandan jihar, Bright Edafe ya ce sun tabbatar da aukuwar lamarin kuma suna bincike a kai.

Ya ce, an tabbatar da mutuwar ne a yayin da aka kai ta wani asibiti domin duba halin da ta shiga.

Ya kuma ce, mijinta na ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma da hannu a mutuwar bisa wasu dalilai.

Kakakin ya kuma ce, sun samu labarin yadda wasu daga cikin iyalan Shimite suke yi wa mijin nata barazanar kai masa hari, lamarin da ya sa ƴan sanda suka kawo shi ofishinsu don ba shi kariya.

A yanzu dai hukumar ta ce tana bincike mai zurfi game da lamarin, inda bayan kammalawa ne za ta fitar da cikakken bayani a kai.

By Babaji