‘Yan Afrika biyu sun shiga sahun waɗanda ka iya maye gurbin Pafaroma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake tsaka da jimamin mutuwar Shugaban Ɗariƙar Katolika ta Kiristocin duniya, Pope Francis da aka fi sani da Pafaroma, an fara tattauna batun wanda zai gaje shi a muƙamin.

Tun gabannin rasuwarsa ne a lokacin da jinyar rashin lafiyarsa ta yi tsananin, Pafaroma ya fara tattaunawa kan wanda zai maye gurbinsa a kujerar.

Waɗanda za su zaɓi sabon shugaban, wato ‘Pope’ sune ƴan tawagar ‘Cardinals’ da suka haɗa da ‘Bishops’ da wasu manyan jami’an Fadar ‘Vatican’

Waɗannan sune suke da damar zama a keɓance domin su tattauna tare da zaɓar wanda zai maye gurbinsa.

Intel region ta ruwaito cewa, an zaɓo ƴan cardinals 15 daga sassa daban-daban na duniya waɗanda daga ciki akwai ƴan Afirka guda biyu, wato Peter Turkson (Ghana) mai shekaru 76, kuma babban jagoran shiyyar Cape Coast.

Sai kuma Fridolin Ambongo Besungu (Jamhuriyar Congo) mai shekaru 65, wanda shi ne babban Bishop na Kinshasa.

Sauran sun haɗa da wasu manyan jagorori daga ƙasashen Italiya, Faransa Amurka da dai sauransu.

By Babaji