Jihar Filato na fama da hare-haren da su ka yi sanadin rasa rayuka 3000 – Gwamna Mutfwang

Spread the love

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa jihar na fuskantar barazana mai tsanani daga ‘yan bindiga, inda ya bayyana cewa sama da mutane 3,000 sun rasa rayukansu a hare-haren da suka faru a cikin ‘yan shekarun nan, musamman a yankin Miango. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke Jos, inda ya jaddada buƙatar ɗaukar matakin haɗin gwiwa domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki a ranar 21 ga Maris, 2023, jihar ta shiga cikin mawuyacin hali na rikici, musamman a ƙananan hukumomin Mangu da Riyom. Ya ce “Mun tashi da safiyar Ranar Kirsimeti da mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 150 a rana ɗaya.” Ya jaddada cewa harin ya nuna cewa matsalar ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai ba, domin masu harin na amfani da muggan makamai.

Haka zalika, gwamnan ya bayyana damuwa kan ayyukan ƙungiyar ta’addanci ta sara suka da ke addabar yankin Jos ta Arewa, inda ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da zuba ido tana kallon irin wannan ɗanyen aiki ba. Ya kuma bayyana cewa jihar za ta yi amfani da duk wata hanya domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

A yayin da aka gudanar da zanga-zanga a Jos a ranar Litinin, ɗaruruwan mutane sun fito ɗauke da alluna suna nuna fushinsu kan yadda gwamnati ke kasa shawo kan kashe-kashen da ke ƙara tsananta. Jagororin addinai da sauran shugabannin al’umma sun buƙaci gwamnati da ta ɗauki gaggawar mataki don kawo ƙarshen wannan bala’i da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.

By ukarofi