
Daga BELLO A. BABAJI
‘Yan bindiga a Zamfara sun sanya tarar Naira miliyan 60 ga ƙauyuka 10 a Ƙaramar Hukumar Maru dake jihar.
Mazauna yankunan sun ce, ƴan bindigar sun yi hakan ne don horar da su bisa zargin su da bai wa sojoji bayanai akan su.
A makon da ya gabata ne sojoji suka farmaki ƴan ta’addar a maɓoyarsu dake yankin dajin Ɗan Kurmi tare da nasarar kashe da dama daga cikin su.
Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaida wa manema labarai cewa ƙauyukan da aka sanya wa harajin sun haɗa da Koloma, Ɗan Hayin Zargado, Zargado, Ɗan Godabe, Sabuwar Tunga, Makini, Bubaka, Yelwa, Bahwada, Koda, Manya, da Kabusu, waɗanda aka yi masu barazanar biyan kuɗaɗen ko kuma a kai masu hari.
Rahotonni sun bayyana cewa, ƴan bindigar sun gayyaci jagororin ƙauyukan ne da fari inda suka tattauna da su game da batun zaman lafiyarsu, wanda sakamakonsa ya ƙare da sanya tarar.
Wani Sarkin gargajiya daga Ɗan Kurmi mai suna Sani Usman ya ce ƴan ta’addar sun kuma ce sun yi hakan ne don hora al’ummar yankunan saboda ƙone dazukan da suka ba su mafaka da suke yi.
