Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Ridda (ko Irtidad) na nufin barin addinin Musulunci a koma wani addinin, ko watsi da addini gabaɗaya, kamar yadda Mulhidai a yau ke yi. A koyarwar fiqihu zaka ji an ce wanda ya bar Musulunci za’a nemi ya dawo har bayan kwana uku, idan ya ki, hukuncinsa kisa ne. To shin haka hukuncin yake Qur’ani, ko a koyarwar Annabi a hadisai? Bari mu fara da Qur’ani.
Cikin Suratul Ma’ida sai Allah ya ce;
Q5:54 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininsa (Musulunci) to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu’i a kan muminai mãsu izza a kan kãfirai”
Kai tsaye babu wata inda-inda Allah ya ce a rabu da Mai Ridda, Allah zai maye gurbinsa da mafificinsa. Sannan a Suratul Ali Imran sai ya ce;
Q3:86-87 “Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu (Ridda) kuma sun yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu? Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. Waɗannan, SAKAMAKONSU shi ne, lalle a kansu akwai la’anar Allah da mãla’iku da mutãne gabã ɗaya”
A nan kuma ya ambaci hukuncinsu shine asara ta Duniya da lahira sakamakon tsinuwar Allah, Mala’iku da mutane. Haka nan dai a cikin surah Al Nahli ya kara da cewa
Q16:106 “Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa (yayi Ridda) fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni. kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma”
A nan ma dai Allah ya jaddada fushinsa da azaba da zata bi mai Ridda, amma babu umarnin a kashe shi. Har yanzu dai a cikin surah Muhammad
Q47:25, 27 & 28 “lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu (Ridda) a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su (Musulunci), Shaiɗan ne ya ƙawãta musu (haka), kuma ya yi musu shibta. To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã’iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu? Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu”
Kamar yadda Allah ke jaddada fushinsa da la’ana a kan masu ridda a ayoyin da suka gabata, a nan kuma sai ya kara da wani hukuncin, cewa ayyukansu sun baci. Wato abinda su ka aikata a Musulunci, sakamakon komawa kafirci ya bata ayyukansu. Sannan a nan ma bai ce a kashe ba sai dai cewa yayin da suka zo mutuwa zasu mutu a azabar Mala’iku.
To, amma duk da tarin wadannan ayoyi, tsawon zamunna, jamhurun malamai a Musulunci na amfani da wasu ayoyi guda biyu na halasta kashe mai Ridda. Amma Allah masani, ya dade da gargadin Musulmi a kan amfani da irin wannan hanya da Malaman su ki bi wajen kawo hukuncin. Wacce hanya ke nan?
Q15:91 “Waɗanda suka sanya Alƙur’ãni gutsure-gutsure”
Ibn Khathir a tafsirin wannan aya ya kawo misalin Malaman Yahudawa da ke daukar wani sashe na littafi domin ya yi daidai da bukatarsu. Ibn Khathir ya ce a Musulmi ma akwai haka inda ya bada misali mai matukar burgewa cewar, Idan aka nunawa mutum bishiya, nan take zai ce bishiya ce, amma idan aka nuna masa, reshe, ko ganyenta, ko itace, ko fure, zai ce bishiya ce? Ya ci gaba da cewa Qur’ani sai an kalli sauran sassa nasa za a fahimce shi, wato tamkar yadda kallon sassan bishiya kadai ba zai baka hotonta ba. Haka nan jamhurun malamai sun yarda da cewa tafsiri mafi inganci shine tafsir Quran fil Quran.
To, dambarwar hukuncin ridda, sai akasarin malamai su ka dauki waccan gurguwar hanyar ta gutsuro wani sashi ba tare da kawo shi gaba daya ba. Bari mu duba ayoyi biyu da su ka yi amfani da su wajen cewa Mai ridda a kashe shi.
1. Surah Al Nisa’i
Q4:89 “Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa’an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki”
Wannan aya ita ce aka zakulo fiqihun cewa duk wanda yayi ridda a nemi ya dawo, idan ya ki, a kashe shi. Malaman sun yi wancan abu da Qur’ani ya kira da “Idhina” wato guggutsura ayoyi. Amma bari mu dinke ayoyin, mu yi musu kallon bishiya maimakon muga reshe ko ganye ko fure, kamar yadda Ibn Khathir ya ambata, mu ga yaya labarin zai tashi? Sai mu faro daga tushen maganar a aya kafin waccan
Q4:88 “To, mẽne ne ya sãme ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi”
Asalin maganar kenan a kan munafukai wadanda su ka yi ridda lokacin yakin Uhud sakamakon sun zame sun gudu suka bar Annabi da Sahabbai a kashe su, su ka koma Madina. Musulmi sai su ka kasu gida biyu; wasu na cewa a kashe su, wasu na ganin kada a yin haka. Sai Allah ya ci gaba da bayanin cewa
Q4:89 “Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa’an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki”
Wato ayar da ake kafa hujja da ita na kashe masu ridda. Allah ya yanke hukunci cewa a bari a koma Madina, idan masu riddar sun tuba sun dawo cikin hanya sai a karbe su. Amma idan sun ki, jininsu ya halatta a kashe su saboda sun zama abokan gaba a bayyane lokacin yaki (enemy combatant) ba wai don kawai sun bar Musulunci ba. A aya ta gaba sai abin ya fita fes
Q4:90 “Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa’an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa’an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu”
To, amma fa ko a cikin wadannan wadanda su ka yi riddar su ka kauracewa Musulmi, idan wani cikinsu ya tafi wajen Banu Nadir ko Qainuqa ko duk wani wanda Annabi ya yi yarjejeniyar Madina (Medinan Constitution) da su, na babu yakar juna, to a rabu da su kada ayi musu komai duk da sun yi ridda. Ko Kuma wadanda su basa nufin yakin Musulmi, ko su yaki kafiran Makka abokan gabar Musulmi, wani abu da zasu iya yi idan sun so hakan, amma sai su ka zabi kada su yake ku, su ka nemi zaman sulhu da ku, sai ayar ta rufe da “To, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu”
Wato wadannan ayoyi a dunkule su na magana ne akan yaki da cin amanar kasa ba wai saboda ridda ba. Domin dada tabbatar da hakan sai a can kuma cikin suratul Ahzab ya ce
Q33:60 “Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu), lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa’an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan”
Wato masu ridda wadanda ke cikin al’umma amma su na mata zagon kasa (spying and spreading sedition) irin wadannan sai Allah ya ce sun zama
Q33:61 “Sunã la’anannu, inda duka aka sãme su a kãmã su, kuma a karkashe su karkashẽwa”
Idan Allah ya tona asirin Dan leken asiri aka kama shi, ayi masa shari’a sannan idan laifinsa ya tabbata, hukuncin kisa ne a kansa. A karshe mu sani cewa ba Musulunci ne ya fara irin wannan hukunci kan masu cin amanar kasa (treasonable felony) ko leken asiri ba (espionage).
Q33:62 “(wannan) Ita ce hanyar Allah (a kan hukunci) a cikin wadanda su ka shude a gabaninka. Kuma ba zaka sami canji ba ga hanyar Allah (hukuncin)”
Duk wanda ya san tarihi, ya san cewa duk wata al’umma Mai tsari da ta shude a baya, ta na yanke hukuncin kisa ne ga duk Dan kasa wanda ya ci amanar kasa, ko bako wanda ya yi leken asiri. Kuma daga nan har karshen Duniya wannan hukunci ba zai canza ba, hukunci ne na Allah da ya zama al’ada ta Dan Adam har wadanda basa addini. A yau duk da tsarin mulhidanci da ya mamaye kafafen iko a Duniya, kusan rabin kasashen Duniya na da hukuncin kisa a kan cin amanar kasa da leken asiri ko daurin Rai da Rai.
A karshe idan muka duba hadisi guda a rayuwar Annabi ya Isa mu gane cewa bai taba bada hukuncin kisa ba domin ridda ko aiwatar da shi a rayuwarsa. Hadisin da Bukhari ya ruwaito a Mujalladi na 4, Littafi na 56, Hadisi na 814. Wanda Anas ya Ruwaito cewa “Akwai wani Kirista wanda ya Musulunta ya na karanta Suratul Baara da Ali Imran, ya kan rubutawa Annabi wahayi. Daga baya yayi ridda ya koma Kiristanci har ya na cewa “Annabi bai san komai ba sai abinda na rubuta masa”. Sai Allah ya karbi ransa, mutanensa su ka binne shi. Amma da safe sai aka ga kasa ta fito da shi…”
A takaice ka ga da hukuncin Ridda kashewa ne da Annabi ya kashe ko ya sa an kashe wannan Sahabi nasa wanda har ya shiga sahun manya irinsu Zaid Bn Thabit, Ali, Usman, Muawiyya, Amr Al’as, Zubar Bn Awwam da sauransu masu rubutawa Annabi Qur’ani.
Zan tsaya nan duk da ban tabo mahimmin bangare ba wanda ya jaddada mana yancin addini ga kowa da Qur’ani ya kawo irinsu:
“la ikhra fid deen”
“Lakum dinikum waliyadin”
“Imma shakiran wa Imma kafura”
“Fa abudu ma shi’itum min dunihi”
Da wasu ayoyin tare da yadda Annabi ya rayu a Makka da Madina. Amma babu wani hukunci na kashe Mai Ridda.
Malam Ali Sadiq manazarci ne kuma marubuci a Kano
